‘Yan Ghana Sun Yi Zanga-Zanga Kan Musgunawa Musulman Rohingya

Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda ake musguna wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a Myanmar

‘Yan Ghana Sun Yi Zanga-Zanga Kan Musgunawa Musulman Rohingya

Wasu daruruwan Musulmai a birnin Accra na kasar Ghana sun gudanar da wata kasaitaciyar zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu da cin zarafin da suka ce ake yi wa Musulmai ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar. Masu zanga-zangar sun kuma nuna rashin jin dadinsu game da abun da suka kira ci gaba da sayar wa […]

Mene ne ya Fusata ASUU ta Soma Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani?

Ranar Lahadi 13 ga watan Agusta, Malaman jami'a a Najeriya suka fara yajin aiki a dukkan jami'o'i mallakin gwamnati.

Mene ne ya Fusata ASUU ta Soma Yajin Aikin Sai Baba-Ta-Gani?

Malaman sun yi haka ne a karkashin kungiyarsu ta malaman jami’o’i, ASUU, inda shugaban kungiyar, Biodun Ogunyemi, ya bayyana wa maneman labarai wannan matakin nasu. Kuma kungiyar ta ce ta yanke wannan shawarar ce bayan da ta tattaro ra’ayoyin mambobinta da ke dukkan jami’o’in kasar, inda ta sha alwashin daina koyarwa da shirya jarrabawa, da […]

Ambaliyar Ruwa Mafi Muni a Afirka a Shekara 20

Birnin Freetown din Saliyo ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa da aka dade ba a ga irin ta ba cikin shekaru masu yawa, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, yayin da wasu daruruwan suka rasa muhallansu.

Ambaliyar Ruwa Mafi Muni a Afirka a Shekara 20

Wannan ambaliyar ruwa ita ce mafi muni da aka fuskanta a nahiyar Afirka cikin shekara 20. Ga dai jadawalin wuraren da ambaliayr ruwa mafi muni ya taba shafa a Afirka; Bala’in sauyin yanayi na El Nino a yammacin Afirka Daga watan Oktobar 1997 zuwa Junairun 1998, fiye da mutum 6,000 ne suka rasu sakamakon ambaliyar […]

Tsohon shugaban kasar Ghana ya gargadi ‘yan Najeriya kan kabilanci

Tsohon shugaban kasar Ghana ya gargadi ‘yan Najeriya kan kabilanci

Tsohon shugaban kasar Ghana Mr Jerry John Rawlings, ya gargadi ‘yan Najeriya kan maganganu wadanda zasu ka iya kawo tashin hankula tare da rarrabuwar kai a kasar a tsakanin al’ummar kasar. Da yake jawabin a jiya a wajen wani taro da kungiyar dalibai ta Jami’ar Ibadan reshen jihar Ekiti ya shirya wanda shine karo na goma […]

Sarauniyar Ingila ta nada dan Ghana a matsayin hadiminta

Sarauniyar Ingila ta nada dan Ghana a matsayin hadiminta

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu ta nada wani dan Ghana a matsayin babban hadiminta wanda zai rika taimakawa wajen kula da harkokin fadarta. Major Nana Kofi Twumasi-Ankrah wanda soja ne da aka haife shi a kasar Ghana. Ya je Birtaniya ne tare da iyayensa a shekarar 1982. Ya yi karatu ne a jami’ar Queen Mary […]