Buhari Ya Taya Jonathan Murnar Cika Shekara 60

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban kasar Goodluck Jonathan murnar cika shekara 60 a duniya.

Buhari Ya Taya Jonathan Murnar Cika Shekara 60

A ranar Litinin ne Mista Jonathan zai cika shekara 60 da haihuwa. Shugaba Buhari ya yaba wa tsohon shugaban inda yake cewa: “ya fara rike mukamin mataimakin gwamna ne, kafin daga bisani ya zama gwamna, kafin ya zama shugaban kasa na tsawon shekara shida, ya fara zama mataimakin shugaban kasa ne”. Daga nan shugaban ya […]

‘Jawabin Buhari Yayi Hannun Riga Da Halin Da Ake Ciki a Nigeria’

Jawabin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a zauren Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata, yana ci gaba da jan hankalin wasu 'yan kasar musamman a shafukan sada zumunta.

‘Jawabin Buhari Yayi Hannun Riga Da Halin Da Ake Ciki a Nigeria’

Yayin da wasu ke ganin cewa shugaban bai yi daidai ba, wasu gani suke ya yi abin da ya kamata. Osasu Igbinedion gani take ya kamata Shugaba Buhari ya warkar da kansa kafin ya nemi bai wa makwabtansa magani. A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, ‘yar Najeriyar ta ce: “Jawabin Buhari a […]

Banida Hannu a Daukar Nauyin IPOB — Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ikirarin da ministan yada labaran kasar, Lai Mohammed, ya yi cewar 'yan hamayya ne ke daukar nauyin kungiyar masu fafatukar kafa kasar Biafra ta IPOB ya nuna cewar har yanzu gwamnatin Buhari na ci gaba da yada farfaganda maimakon mayar da hankali kan aiki.

Banida Hannu a Daukar Nauyin IPOB — Jonathan

A wata sanarwar da Reno Omokri, mataimaki na musamman kan shafukan sadarwar zamani ga Shugaba Goodluck Jonathan, ya wallafa a shafin Facebook na tsohon shugaban kasar, cewa idan gwamnatin Najeriya ta san ‘yan hamayyar da ke daukar nauyin ‘yan IPOB, ta kama su tare da gurfanar da su gaban kotu. Mista Jonathan ya ce bai […]

Jonathan ya soki Buhari kan Zakzaky

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce gwamnatin Najeriya ba ta aiki da umarnin kotu, inda ya buga misali da yadda ta ki sakin wadansu mutanen da take rike da su.

Jonathan ya soki Buhari kan Zakzaky

“Muna so ‘yan Najeriya su lura cewa kotuna sun bayar da umarni ga gwamnati ta saki Kanar Sambo Dasuki da Sheikh Ibrahim el-Zakzaky, a matsayin beli, amma an ci gaba da tsare su. A fili take cewa gwamnatin APC tana zabar irin biyayyar da za ta yi wa kotu”, in ji Mista Jonathan. Ya ce […]

Matasan Najeriya sun yi fushi matuka – Obasanjo

Matasan Najeriya sun yi fushi matuka – Obasanjo

Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya shaida wa BBC cewa matasan kasar na cike da fushi shi ya sa ake samun kiraye-kiraye na raba kasar. Cif Obasanjo ya ce “Matasa a kowanne yanki na Najeriya: gabas da yamma, kudu da arewa, suna cikin damuwa shi ya sa muke nema mafita ta kowacce hanya”. A […]

Jonathan ya shaida cewar shi ne wanda aka fi suka a duniya

Jonathan ya shaida cewar shi ne wanda aka fi suka a duniya

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mayar da martani ga yunkurin gwamnatin kasar na yin dokar da ta haramta furta kalaman nuna kiyayya tsakanin al’ummomin kasar. Mista Jonathan ya sake wallafa wani hoto a shafinsa na Facebook wanda ya yake dauke da rubutu kamar haka: “Ni ne shugaban da aka fi zagi da suka a […]

Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?

Rawar da Farfesa Yemi Osinbajo yake takawa a matsayin mukaddashin shugaban kasa sakamakon rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya shafe watanni a wajen kasar na ci gaba da jan hankalin jama'a. Yayin da wasu ke cewa yana taka rawar gani, wasu kuwa cewa suke yi yana dari-dari.

Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?

Rashin lafiyar shugaban, wanda ba a bayyana takamaiman abin da ke damunsa ba, da kuma halin da kasar ke ciki ya sa fagen siyasar kasar daukar dumi a wasu lokuta. Akwai wadanda suke ganin babu abin da ya sauya bayan da Mista Osinbajo ya fara tafiyar da kasar a watan Janairun da ya gabata. Masu […]

An kori ‘yan sandan da ‘suka wawushe gidan Jonathan’

Rundunar 'yan sandan babban birnin Najeriya, Abuja, ta kori 'yan sanda hudu da ake zargi da hannu a wawushe wani gidan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, da ke unguwar Gwarimpa a Abuja.

An kori ‘yan sandan da ‘suka wawushe gidan Jonathan’

Wata sanarwar da rundunar ta fitar ta ce bayan an gudanar da bincike kuma an samu ‘yan sandan da ke gadin gidan tsohon shugaban kasan da hannu cikin satar da aka yi a gidan, kwamishinan ‘yan sandan birnin, CP Musa Kimo, ya amince da korar ‘yan sandan hudu. Wadanda aka kora din sun hada da […]

Barayi ‘sun wawashe’ gidan Goodluck Jonathan na Abuja

Barayi ‘sun wawashe’ gidan Goodluck Jonathan na Abuja

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya ce barayi sun shiga gidansa da ke unguwar Gwarinpa a babban birnin kasar Abuja, inda suka yi masa sata ta hanyar dauke duk wani abu da za su iya a gidan. A wata sanarwa da mai magana da yuwunsa Ikechukwu Eze ya fitar, ya ce a watan da […]

‘Yan Nijeriya Na Bukatar Jam’iyyar PDP A Zaben 2019, Cewar Jonathan

‘Yan Nijeriya Na Bukatar Jam’iyyar PDP A Zaben 2019, Cewar Jonathan

Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya ce, ‘yan Nijeriya na bukatar jam’iyyar adawa ta PDP da ta dawo ta cigaba da mulkin kasar nan a shekarar 2019. Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jiya Litinin yayin tattaunawar da shugabannin jam’iyyar su ka yi a babbar sakatariyyar jam’iyyar “Wadata Plaza” da ke Abuja. […]