An sace gwamman mutane a Kaduna

Rahotanni daga Birnin Gwari a jihar Kaduna a Najeriya na cewa 'yan bindiga sun sace fiye da mutum 80 a kan wata babbar hanya.

An sace gwamman mutane a Kaduna

Jami’an Kula da Motocin Haya ta NURTW, sun ce an sace mutanan ne a kan wata babbar hanya da ta hada arewaci da kudancin kasar. Mazauna da jami’an sufuri a yankin Birnin-Gwari sun ce a ranar Lahadi ne ‘yan bindiga suka tsayar da motoci da dama, suka sace dumbin matafiya tare da shigar da su […]

Yunkurin Jihar Kaduna Na Ciwo Bashi Ya Haddasa Yamutsi

Jihar Kaduna na cikin jihohin da suke neman ciwo bashi amma wannan lamarin ya rarraba kawunan ‘yan jihar inda har mata suka fito suna zanga zanga tare da dorawa Senator Shehu Sani laifin kawo cikas ga yunkurin

Yunkurin Jihar Kaduna Na Ciwo Bashi Ya Haddasa Yamutsi

Yunkurin gwamnatin jihar Kaduna na ciwo bashi domin gudanar da wasu ayyuka na ci gaba da rarraba kawunan ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar. Wasu mata da suka dorawa Senator Shehu Sani alhakin jawo jinkirin ciyo bashin sun fito sun yi zanga zanga a garin Kaduna, babban birnin jihar. Daya daga cikin matan da suka […]

Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya

Rikicin kabilanci da addini a kudancin jihar Kaduna ya sabbaba asarar rayuka

Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya

A duk shekara, majalisar dinkin duniya na ware ranar 21 ga watan Satumba domin kara fadakar da al’umma muhimmacin zaman lafiya a duniya. Jihar Kaduna a tarayyar Najeriya na cikin jihohin da suka yi fama da rikice-rikice masu nasaba da addini, kabilanci, ko siyasa. Bisa la’akari da wannan ranar ne wakilinmu Aminu sani Sado a […]

An Yi Gangamin Ilimantar da Jama’a Kan Illar Ambaliyan Ruwa

Yau a Kano hukumar kula da harkokin ruwa ta najeriya ta gudanar da taron ganganmin wayar da kan jama’a dangane da hanyoyin kaucewa annobar ambaliyar ruwa.

An Yi Gangamin Ilimantar da Jama’a Kan Illar Ambaliyan Ruwa

Hukumar kula da harkokin ruwa da yanayi ta Najeriya ta gudanar da taron yawar da kawunan jama’a akan illar ambaliyan ruwa Taron ya kunshi masu ruwa da tsaki da suka hada da masana kan lamuran albarkatun ruwa da raya gandun daji, da kwararraru kan harkokin muhalli da sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati kan sha’anin tsara […]

Matar Da Aka Sace Da ‘Yarta A Sokoto An Same Su A Kaduna

Matar Da Aka Sace Da ‘Yarta A Sokoto An Same Su A Kaduna

Lokaci ne na jimami ga iyalan wata matar aure mai shekaru 26, mai suna Sa’adatu Umar Abubakar, inda ranar Litinin 4 ga watan Satumbar shekarar da muke ciki ta 2017 aka sace matar da ‘yarta a Sokoto kan hanyar su ta zuwa bikin radin suna a gidan wasu ‘yan uwansu dake cikin garin na Sokoto. […]

Gwamna El-Rufai ya samar da sabbin kayan aiki a babban asibitin Kafanchan

Gwamna El-Rufai ya samar da sabbin kayan aiki a babban asibitin Kafanchan

Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagoracin Mallam Nasir el-Rufai ta samar da sabbin kayayyakin aiki na zamani a babban dakin shan magani na jihar ta Kaduna dake garin karamar hukumar Kafanchan. Sanarwar ta biyo baya a yau ta shafin sada zumunta na jihar wanda kanyi bayani akan ci gaban da gwamnatin kan samu a yau da […]

Hadaddiyar kungiyar matasan arewaci Nigeria ta janye umarnin korar yan kabilar Igbo bisa wasu sharudda

Hadaddiyar kungiyar matasan arewacin Nigeria ta janye umarnin korar yan Kabilar Igbo daga arewacin kasar, amma ta gitta wasu sharudda.

Hadaddiyar kungiyar matasan arewaci Nigeria ta janye umarnin korar yan kabilar Igbo bisa wasu sharudda

Matasan arewacin Nigeria su dakatar ko kuma sun janye umarta ‘yan kabilar Igbo su tashi daga arewa su koma yankinsu na kudu maso gabashin kasar kan ranar daya ga watan Oktoba. A wani gagarumin taro a Abuja, hadaddiyar kungiyar matasan tace ta dau wannan mataki ne saboda kiraye kiraye da dattawan yankin suka yi da […]

An Yanka Ta Tashi a Kan Maganar Wa’adi Ga ‘Yan Kabilar Igbo

Gamayyar kungiyoyin matasan Najeriyar nan da su ka ba wa 'yan kabilar Igbo wa'adi na su bar arewacin kasar kafin ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, sun sanar da janyewar wa'adin da suka bayar .

An Yanka Ta Tashi a Kan Maganar Wa’adi Ga ‘Yan Kabilar Igbo

Hadakar kungiyoyin ta sanar da janye wa’adin ne a wani taro da ta gudanar a Abuja babban birnin tarrayar kasar da yammacin ranar Alhamis. A dai cikin watan Yuli ne hadaddiyar kungiyar matasan arewacin Najeriyar suka fitar da wata sanarwa a Kaduna, inda a ciki suka bayar da wa’adi har zuwa ranar daya ga watan […]

Me Ya Sa Jiragen Sojin Nigeria Ke Yawan Hatsari?

A ranar Alhamis ne wani karamin jirgin yakin sojin saman Najeriya ya yi hatsari a Kaduna da ke arewacin kasar, a lokacin da yake wani aiki.

Me Ya Sa Jiragen Sojin Nigeria Ke Yawan Hatsari?

A ranar Alhamis ne wani karamin jirgin yakin sojin saman Najeriya ya yi hatsari a Kaduna da ke arewacin kasar, a lokacin da yake wani aiki. A wata sanarwa da rundunar sojin saman kasar ta aikewa manema labarai ta ce, matukin jirgin wanda shi kadai ne a ciki lokacin da hatsarin ya afku ya mutu. […]

Hukumar SSS Ta Damke Wasu Kwamandojin Kungiyar Boko Haram

Hukumar tsaron farin kaya ta SSS a Najeriya ta ce jami’anta sun damke wasu manyan kwamandojin Boko Haram a jihohin Kano da Kaduna da Taraba.

Hukumar SSS Ta Damke Wasu Kwamandojin Kungiyar Boko Haram

WASHINGTON D.C. —  Cikin wata sanarwa da hukumar SSS ta aikawa manema labarai, hukumar ta ce ta cafke wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram mai suna Usman Musa a garin Sakwai dake karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna. Hukumar dai ta ce ta kama kwamandan ne tare da wasu mayakan Boko Haram, da suka hada […]

1 2 3