Da Izinin Iyayena Na Fara Fim – Maryam Yahya

Tauraruwar matashiyar jaruma Maryam Yahaya, mai shekara 20, ta fara haskawa ne a cikin fim dinta na farko wato Mansoor.

Da Izinin Iyayena Na Fara Fim – Maryam Yahya

A wata hira da Yusuf Ibrahim Yakasai, ta shaida masa ta taka rawar babbar jaruma a fim din duk da cewa shi ne fitowarta ta farko a fina-finan Kannywood, saboda ta kudurci aniyar taka rawar da masu shirya fim din suka umarce ta duk da kasancewarta sabuwar fitowa. Ta kara cewa ainahi ba ita ce […]

‘Dan autan’ mawakan hip hop na Hausa Lil Ameer ya rasu

‘Dan autan’ mawakan hip hop na Hausa Lil Ameer ya rasu

Lil Ameer, wanda ake yi wa lakabi da dan autan mawakan hip hop na Hausa ya rasu. Mawakin, wanda ya yi fice a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ya rasu ne sakamakon hatsarin mota. Lil Amir ya yi wakoki da dama kuma masana harkokin fina-finan Kannywood irin su Farfesa Abdallah In a Adamu sun […]

An Gudanar da Jana’izar Kasimu Yero a Kaduna

An Gudanar da Jana’izar Kasimu Yero a Kaduna

An gudanar da jana’izar marigayi Alhaji Kasimu Yero a jiya bayan rasuwar sa a ranar Lahadin data gabata a gidan sa dake a unguwar Magajin Gari a birnin na Kaduna. Alhaji Kasimu Yero mai shekaru 70 a duniya ya rasu a jiyan da rana a birnin Kaduna dake arewacin Najeriya bayan ya sha fama da […]

Dalilin da ya sa ake min kallon ‘yar wiwi — Hauwa Waraka

Dalilin da ya sa ake min kallon ‘yar wiwi — Hauwa Waraka

Jarumar fina-finan Hausa, Hauwa Abubakar wacce aka fi sani da Hauwa Waraka, ta ce tana yawan fitowa a mutuniyar banza ne saboda ta nunawa al’umma illar rashin kirki. “Ina fitowa a matsayin karuwa ko ‘yar kwaya ko ballagaza ne saboda na ilimantar da mutane domin su guji zama irin wadannan mutane”, in ji Hauwa Waraka, […]

Dalilin da ya sa nake boye wasu abubuwa da suka shafe ni – Nafisa Abdullahi

Ina da dalilaina na boye wasu abubuwan da suka shafi lamari irin wannan kafin a kammala. A wasu lokutan, idan ka bayyana abu, a karon farko sai ka ga ka rage wa mutane karsashi.

Dalilin da ya sa nake boye wasu abubuwa da suka shafe ni – Nafisa Abdullahi

Kwana biyu an ji ki shiru a finafinai, ko lafiya? To, gaskiya ba zan ce an ji shiru ba, kawai dai hutu ne kamar yadda kowa yake yi. Kuma na yi hakan ne domin na mayar da hankali kan sabon fim dina da yanzu haka muke shiryawa, yana nan fitowa nan ba da jimawa ba. […]

Fim Ne Ya Hana Ni Zama Farfesa — Bosho

Fitaccen dan wasan barkwanci na fina-finan Hausa Sulaiman Yahaya, wanda aka fi sani da Bosho ya ce tsundumar da ya yi cikin harkar fim ce ta hana shi zama farfesa.

Fim Ne Ya Hana Ni Zama Farfesa — Bosho

“Na samo sunan Bosho ne saboda lokacin da nake makarantar sakandare ina yawaita karatu. Na kan kwashe kwana 40 ban yi cikakken bacci ba saboda yawan karatu. “Shiga ta harkar fina-finai ce ta hana ni zama farfesa,” in ji Bosho, a hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa. Dan wasan ya ce sha’awarsa […]

‘Babu wanda zai sake lashe gasa idan ina Kannywood’

Fitaccen jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq ya ce kwarewarsa ta iya taka kowacce rawa ce ta sa ya lashe gasar jarumin jarumai sau uku a jere.

‘Babu wanda zai sake lashe gasa idan ina Kannywood’

“Idan har Ina cikin Kannywood ni ne zan ci gaba da lashe gasar jarumin jarumai a ko wacce shekara saboda ba na wasa da aikina”, in ji Sadiq Sani Sadiq, a tattaunawa ta musamman da BBC Hausa. Ya musanta zargin da ake yi cewa yana jajircewa a fim ne domin ya dusashe taurarin jarumai Ali […]

Dalilin da ya sa na fito a Barauniya – Hafsa Idris

Jarumar fina-finan Kannywood Hafsa Idris, ta ce wata shida ta kwashe tana karanta rubutaccen labarin "Barauniya" shi ya sa ta taka rawa sosai a fim din kamar yadda gogaggun barayi ke yi.

Dalilin da ya sa na fito a Barauniya – Hafsa Idris

Hafsa, wacce ake kira ‘Barauniya’ ko ‘Yar Fim a Kannywood, ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ta soma fim ne domin ba ta son zaman banza. Ta kara da cewa, “Yin fim ya fi aikin gwamnati domin kuwa abin da nake samu ma’aikacin gwamnati ba zai samu ba.” Da fim nake yin hidimomina da na iyayena […]

An hana ni aure saboda zargin luwadi – Adam A Zango

Na yi nadamar fitowa a akasarin fina-finan da na yi — Adam Zango

An hana ni aure saboda zargin luwadi – Adam A Zango

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango, ya ce babban burinsa shi ne ya kware wajen magana da harshen Turanci. Zango, wanda aka haifa a garin Zangon Kataf na jihar Kaduna, ya yi karatun sakandare a birnin Jos na jihar Plateau ne. Jarumin ya ce zai bar sana’arsa nan da dan wani lokaci domin ya […]

Kannywood: ‘Satar fasaha na matukar illata sana’armu’

Kannywood: ‘Satar fasaha na matukar illata sana’armu’

Masu ruwa da tsaki a fagen fina-finan Kannywood sun dade suna kokawa kan batun satar fasaha da suka ce tana kassara sana’arsu, to ko yaushe za a kawo karshen wannan halayyar ta bera? Satar fasaha wata hanya ce ta ci da gumin wani ko wasu. A takaice, satar fasaha na nufin sace wani aiki da […]