Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Duba Tsarin Albashin Ma’aikata

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin mutane 30, wadanda zasu yi nazari da yin tsari na sabon tsarin albashin ma’aikatan kasar mafi kankanta, daga Naira dubu 18 da yake a yanzu zuwa wani kima da ya wuce haka.

Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Duba Tsarin Albashin Ma’aikata

A lokacin da shugaba Buhari ke kaddamar da kwamitin wanda ya hada da gwamnoni da ministoci da kungiyoyin kwadago da na ma’aikata, ya ce wajibi ne a kafa wannan kwamiti a dai-dai lokacin da Najeriya ke ganin lokaci yayi ta bi jerin kasashen duniya, da za a inganta tsare-tsaren albashi na ma’aikaci saboda muhimmancin sa […]

Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

A ranar Laraba ne kwale-kwale ɗauke da 'yan kasuwa 150 daga kauyen Gaya cikin jamhuriyar Nijar da ke kan hanyar zuwa kasuwa a garin Lolo a jihar Kebbi ya kife.

Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

An samu ceto mutane 50 daga cikinsu. Har yanzu ma’aitakan ceto daga jamhuriyyar Nijar da Najeriya na ci gaba da aikin ceton waɗanda suka rage. Sai dai babu tabbas cewa za’a same su a raye. A halin yanzu an kai wadanda aka ceto asibitin Lolo domin samun magunguna da kulawa. Jami’an hukumar bada agajin gaggawa […]

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Hada Jihohi Uku da Layin Dogo

Ministan sufuri Amaechi ya fada a Sokoto gwamnatin tarayya na shirin hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo irin na zamani

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Hada Jihohi Uku da Layin Dogo

Kokarin gwamnatin tarayyar Najeriya na hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo ba zai tabbata ba sai da amincewar Majalisar Dattawa a cewar ministan sufurin kasar. A cewarsa tuni gwamnati ta tura bukatar zuwa majalisar. Rotimi Amaechi wanda shi ne ministan sufuri a karkashin shugabanci Muhammad Buhari yace jihohin uku da ake son […]

An Kaddamar da Kamfanin Sarrafa Shinkafa a Jihar Kebbi

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a yankin Afrika ta Yamma a Argungu ta jihar Kebbi.

An Kaddamar da Kamfanin Sarrafa Shinkafa a Jihar Kebbi

Yace shirye shiryen gwamnatin tarayya a kan noma da habbaka tattalin ariziki sun fara samun nasara. Shekaru biyu da suka gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da noman shinkafa a jihar Kebbi bisa sabo tsarin gwamnatinsa na fadada kafofin tattalin arzikin kasar da kuma rage dogaro akan albarkatun man fetur ta hanyar habbaka sha’anin […]

PDP: ‘An tsawwala kudin fom din zabe a Kebbi’

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato PDP ta ce ba za ta iya shiga zabukan majalisun kananan hukumomi da za a yi a jihar Kebbi a yawancin wurare ba saboda karancin kudi.

PDP: ‘An tsawwala kudin fom din zabe a Kebbi’

Idan an jima dai ne za a bude rumfunan zabe domin zaben shugabannin da kansiloli na kananan hukumomin jihar 21. Jam’iyyar dai ta ce ta tsayar da ‘yan takarar shugabancin ne a kananan hukumomin shida kacal. Ibrahim Umar Ummai shi ne sakataren watsa labaran ta, Sakataren yada labaran jam’iyyar ya shaidawa BBC cewa hukumar zaben […]