An kai karar Kim Kardashian saboda satar jakar selfie

An kai karar kamfanin Kim Kardashian West saboda satar fasahar jakar selfie.

An kai karar Kim Kardashian saboda satar jakar selfie

Jakar saka wayar komai-da-ruwanka ta LuMee, wacce kamfanin Kimisaprincess Inc ke tallatawa, tana da wata fitila da ke taimakawa masu amfani da ita wurin daukar hoton dauki-da-kanka, selfie, mai kyau. Amma wani mutum mai suna Hooshmand Harooni ya bukaci ta biya shi $100m (£75m) saboda satar fasaharsa. Ya ce shi ne ya “kirkiro fitila da […]