An Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi A Legas

Ambaliyar ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kawo cikas ga zaben kanana hukumomi a wasu yankunan birnin Legas.

An Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi A Legas

A yau aka gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Legas kuma zaben ya tafi dai dai yadda aka tsara a wasu yankuna na birnin Legas,inda ba a samu ambaliyar ruwa ba. Rahotani na nuni da cewa jama’a sun fito sosai domin jefa kuri’arsu, amma akwai rahotani dake cewa ba a samu fitowar mutane da […]

Basarake ya kitsa shirin sace kansa a matsayin garkuwa

Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya dakatar da Yusuf Ogundare, wanda shi ne basaraken Shangisha a Magodo da ke cikin jihar Legas saboda kitsa shirin sace kansa da kaninsa a matsayin garkuwa.

Basarake ya kitsa shirin sace kansa a matsayin garkuwa

A ranar 5 ga watan Yuli ne basaraken ya bace a cikin karamar hukumar Ikosi-Isheri ta jihar Legas. A sanadiyyar wannan ne gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya dakatar da basaraken daga aiki. A wata sanarwar da kwamishinan kananan hukumomi da al’ummomi ya sanya wa hannu, ta ce gwamnan ya dakatar da basaraken daga aikinsa. […]

Ambaliyar ruwa ta tsayar da al’amura a Lagos

Al'amura sun tsaya cak, yayin da mutane suka kasance a gida a wasu sassan birnin Legas da ke kudancin Najeriya, bayan wani ruwansa da aka kwashe kwanaki ana yi ya haddasa ambaliyar ruwa.

Ambaliyar ruwa ta tsayar da al’amura a Lagos

Mazauna unguwannin Lekki da Victoria Island sun wari gari ranar Asabar da ambaliyar ruwa bayan kwashe kwana biyar a ruwa, kamar yadda wata wadda take zaune a Legas ta shaida wa BBC. “Yau kwana biyar ke nan ana ruwa babu dauke wa a unguwar Lekki. Ko ‘ya’yanmu ma a cikin ruwa suke zuwa makaranta cikinsa […]

Kotu ta umarci gwamnati ta biya diyyar rushe gidaje

Kotu ta umarci gwamnati ta biya diyyar rushe gidaje

Wata babbar kotu a Legas, babban birnin kasuwanci na Najeriya ta yanke hukunci a kan shari’ar da fiye da mutane 30,000 suka shigar game da rushe gidajensu da gwamnati ta yi. Gwamnatin jihar Legas dake kudu maso yammacin Najeriya ta tashi unguwar marasa galihu ta Otodo Gbame daga watan Nuwambar 2016 zuwa watan Fabrairun bana. […]