‘Yan Boko Haram Sun Kashe Manoma Biyu, Sun Sace Biyu

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun shiga wani kauye mai suna Alau mai tazarar kilomita biyar daga Maiduguri, babban birnin jahar Borno, su ka yi ma wasu manoma biyu yankar rago su ka kuma sace wasu biyu.

‘Yan Boko Haram Sun Kashe Manoma Biyu, Sun Sace Biyu

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun shiga wani kauye mai suna Alau mai tazarar kilomita biyar daga Maiduguri, babban birnin jahar Borno, su ka yi ma wasu manoma biyu yankar rago su ka kuma sace wasu biyu. Tashin hankalin da ya biyo bayan wannan al’amari ya sa wasu magabatan wannan gari, […]

Ana Zargin Wani Dan Sanda Da Kashe Kansa Saboda Sauya Masa Gurin Aiki Zuwa Maiduguri, ‘Yan Sanda Sun Karyata Zargin

Ana Zargin Wani Dan Sanda Da Kashe Kansa Saboda Sauya Masa Gurin Aiki Zuwa Maiduguri, ‘Yan Sanda Sun Karyata Zargin

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi sun karyata labarin dake kewayawa garin Abakaliki cewa daya daga cikin ‘yan sandan jihar ya kashe kansa ranar Litinin saboda sauya masa gurin aiki zuwa Maiduguri. ASP. Loveth Odah, Maimagana da Yawun ‘Yan Sandan Jihar ya fadawa manema labarai ranar Talata cewa Oyibe bai kashe kansa da gangan ba  kamar […]

Hukumar Tashar Jiragen Ruwa Ta Sake Gina Wasu Makarantun Sakandare a Borno

Rikicin Boko Haram da Jihar Borno ta samu kanta ciki ya lalata makarantu da yawa sabili da haka ne Hukumar Tashar Jiragen Ruwan Najeriya ta soma sake gina makarantun inda ta mikawa gwamnatin jihar guda uku da ta kammala cikin birnin Maiduguri.

Hukumar Tashar Jiragen Ruwa Ta Sake Gina Wasu Makarantun Sakandare a Borno

Hukumar Tashar Jiragen Ruwa ta Najeriya ta gyara ko sake gina wasu makarantu uku da rikicin Boko Haram ya rutsa dasu. Hukumar tace ta zabi gudanar da aikin ne domin ba da tata gudummawa ga al’ummar jihar Borno da kuma taimakawa harkokin ilimi a tarayyar Najeriya. Alhaji Balarabe Umar Samaila babban daraktan hukumar wanda kuma […]

Sama da yara dubu 56 sun daina makaranta a Najeriya

Sama da yara dubu 56 suka rasa iyayensu sanadiyyar rikicin Boko Haram a Maiduguri, lamarin daya tilasta musu barin makarantu tare da neman sana'o'in da za su rike kansu da su.

Sama da yara dubu 56 sun daina makaranta a Najeriya

Sama da yara dubu 56 suka rasa iyayensu sanadiyyar rikicin Boko Haram a Maiduguri, lamarin daya tilasta musu barin makarantu tare da neman sana’o’in da za su rike kansu da su.A Najeriya, gwamnatin jihar Borno ta ce sama da kananan yara dubu 56 ne ta tabbatar da cewa sun rasa iyayensu sakamakon rikicin Boko Haram, […]

“Dole gwamnatin Najeriya ta kare ‘yan gudun hijira”

Hukumar jin-kai ta duniya ta bayyana cewa, dole ne gwamnatin Najeriya ta inganta matakan tsaro don kare lafiyar mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

“Dole gwamnatin Najeriya ta kare ‘yan gudun hijira”

Wannan na zuwa ne bayan mutane 28 sun rasa rayukansu sakamakon wani kazamin hari da ake zargin Boko Haram da kai wa a sansanin ‘yan gudun hijirar a yammacin jiya Talata. Hukumar ta ce, sansanin ‘yan gudun hijira, wani tudun mun-tsira ne ga mutanen da suka guje wa tashin hankali , amma kuma saboda sakaci, […]

Boko Haram ta kashe mutane kasuwar Konduga

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, kungiyar Boko Harm ta kaddamar da hare-haren kunar bakin wake a karamar hukumar Konduga, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 27.

Boko Haram ta kashe mutane kasuwar Konduga

Maharan su tayar da bama-bamai guda biyu a wata kasuwa da ke karamar hukumar kuma a dai dai lokacin da jama’a ke tsaka da cin kasuwancinsu a yammain wannan Litinin kamar yadda wakilinmu, Bilyaminu Yusuf ya tabbatar mana. Bam na uku ya tashi ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin na Kondugan kamar […]

Harin kunar bakin wake ya kashe mutum 20 a Nigeria

Rahotanni daga jihar Bornon Najeriya na cewa akalla mutane 20 ne suka mutu sannan fiye da 30 suka samu munanan raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake a garin Konduga.

Harin kunar bakin wake ya kashe mutum 20 a Nigeria

Wasu mata ne guda uku suka kai harin a wata kasuwar sayar da raguna da ke unguwar Mandirari da yammacin ranar Talata. An ce guda biyu daga cikin matan sun kai ga tayar da bama-baman da ke jikinsu, a inda jami’an tsaro suka harbe ta ukun kafin ta tayar da nata. Matan sun kasu gida […]

Sojojin Najeriya Sun Kutsa Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Maiduguri

Yau da misalin karfe biyar na safiya wasu sojojin Najeriya suka kutsa cikin ofishin Majalisar Dinkin Duniya ko MDD dake Maiduguri ba tare da izinin ba

Sojojin Najeriya Sun Kutsa Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Maiduguri

Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta tabbatar da cewa rundunar sojojin Najeriya ta kutsa cikin ofishinta dake Maiduguri da misalin karfe biyar na asuba ba tare da samun izinin ba. A sanarwar da ta aikawa manema labarai MDD ta ce sojojin sun afka ofishinsu ne inda suka kuma gudanar da bincike ba tare da shsaida […]

Neman ‘yan Boko Haram ne ya kai mu ofishin MDD – Sojin Nigeria

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun gudanar da bincike kan gida 30 ciki har da wani ginin Majalisar Dinkin Duniya don neman wasu manyan 'yan Boko Haram a Maiduguri.

Neman ‘yan Boko Haram ne ya kai mu ofishin MDD – Sojin Nigeria

Ta ce binciken ya biyo bayan wasu sahihan bayanai da ta samu cewa wasu manyan ‘yan Boko Haram sun yi satar shiga yankin Pompomari Bye Pass. Sanarwar wadda rundunar ta fitar ranar Juma’a a Maiduguri ta ce a tsawon mako guda da ta yi tana aikin killacewa da bincike, ta bankade unguwannin a Jiddari – […]