‘Yan Najeriya Na Mayar da Martani Kan Kafa Dokar Hana Kalamun Batanci

A cikin wata sanarwa jiya shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ya ce zasu mayar da hankali wajen kafa dokar hana kalamun batanci da dokar hana mutane aiwatar da shari'a da kansu maimakon su bar kotu ta yanke hukumci.

‘Yan Najeriya Na Mayar da Martani Kan Kafa Dokar Hana Kalamun Batanci

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya fada cikin wata sanarwa jiya cewa kudurorin hana kalamun batanci da na daukan hukumci a hannu zasu sami kulawar da ta kamata domin su zama dokoki cikin karamin lokaci. Inji Sanata Saraki hakan nada nasaba da yadda kalamai da lafuza dake kara dumama yanayi ke ci gaba […]