Kasashen Duniya Na Dabda Sanya Hannu Don Haramta Nukiliya

Kasashen duniya 51 sun shirya tsaf don sanya hannun kan wata yarjejeniya da za ta haramta mallakar makamin Nukiliya a duniya, abin da Amurka da sauran kasashen da suka mallaki irin wannan makamin ke matukar adawa da shi.

Kasashen Duniya Na Dabda Sanya Hannu Don Haramta Nukiliya

Wannan dai na zuwa ne a yayin da rikickin nukiliyar Koriya ta Arewa ke dada kamari, lura da yadda ta ke ci gaba da gwaje-gwajen makamin duk da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba ma ta. Kimanin kasashe 122 ne suka goyi bayan assasa dokar ta haramta mallakar makamin a wani taron Majalisar Dinkin […]

Girgizar kasa ta hallaka sama da mutum 200 a Mexico

Wata mummunar girgizar kasa ta faru a tsakiyar birnin Mexico, inda ta hallaka mutane sama da 200, yayin da dama suka jikkata, wasu kuma ta rutsa su a cikin buraguzan gine-gine da suka rushe

Girgizar kasa ta hallaka sama da mutum 200 a Mexico

Girgizar wadda ta kai karfin lamba 7.1 a ma’aunin girgizar kasa, ta rushe gomman gine-gine, a babban birnin kasar, Mexico City, wadanda suka hada da wata makaranta, inda ake ganin ta rutsa yara a ciki. Tarin masu aikin sa-kai sun shiga taimaka wa masu aikin ceton gaggawa a kokarin da ake yi na gano masu […]

Zakarun Nahiyoyi: Chile ta yi waje da Portugal da 3-0

Zakarun Nahiyoyi: Chile ta yi waje da Portugal da 3-0

Chile ta yi waje da Portugal a wasan kusa da karshe na cin kofin zakarun nahiyoyi da ci 3-0 a bugun fanareti a gasar da ake yi a Rasha. Bayan minti 90 da kuma karin minti 30 na fitar da gwani, ba kasar da ta zura kwallo, hakan ya sa aka je bugun fanareti. Chile […]

Zakarun Nahiyoyi: Kamaru ta yi 1-1 da Australia

Zakarun Nahiyoyi: Kamaru ta yi 1-1 da Australia

Kamaru ta yi kunnen doki 1-1 da Australia a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha a ranar Alhamis din nan. Zakarun na Afirka su ne suka fara jefa kwallo a raga ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, ta hannun Zambo Anguissa. Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin ne kuma […]

Kofin Zakarun Nahiyoyi : Chile da Jamus sun yi 1-1

Kofin Zakarun Nahiyoyi : Chile da Jamus sun yi 1-1

Jamus da chile su ka tashi kunnen doki 1-1 a wasan cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha a ranar Alhamis din nan. Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez shi ne ya ci wa Chile kwallonta minti shida da fara wasa bayan da Arturo Vidal na Bayern Munich, ya zura masa kwallon da dan […]