An Gurfanar da Maharan Barcelona Gaban Kotu

Daya daga cikin Maharan birnin Bercelona da aka gurfanar da su yau gaban kotun Madrid babban birnin kasar Spain ya shaidawa kotu cewa suna shirye-shiryen kaddamar da wani gawurtaccen hari a kasar nan gaba kadan.

An Gurfanar da Maharan Barcelona Gaban Kotu

Da safiyar yau ne dai aka gurfanar da mutanen hudu da a ke zargi da hannu a tagwayen hare-haren na Bercelona gaban kotun da ke Madrid babban birnin kasar don amsa tuhuma, baya da ‘yan sanda suka halaka guda cikinsu a jiya wato Younes Abouyaaqoub lokacin da yake kokarin tserewa daga garin. Maharin wanda aka […]