Kotu Ta Yankewa Wani Da Yayi Fashin Naira 3,420 Hukuncin Rataya

Wata babbar kotu dake birnin Osogbo na jihar Osun ta yankewa wani matashi hukunci kisa, bayan samunsa da laifin yiwa wata mata fashi da makamin Naira 3,420.

Kotu Ta Yankewa Wani Da Yayi Fashin Naira 3,420 Hukuncin Rataya

  Kotu ta yankewa Kayode Adedeji hukuncin rataya bayan da ta same shi da laifin aikata fashi da makami. Adedeji dai ya yiwa Omowumi Adebayo fashi da wuka cikin dare inda ya karbe mata kudi har Naira 3,420. Duk da yake masana shari’a na ganin hukuncin da kotun ta yanke ba wani abin mamaki bane, […]

Najeriya ta karbi Jirayen Yaki 5 daga Pakistan

Najeriya ta karbi Jirayen Yaki 5 daga Pakistan

Rundunar Sojin saman Najeriya ta karbi wasu sabbin jiragen yaki guda biyar. Wani katon jirgin dakon kaya ya sauka a tsohon filin sauka da tashin jiragen sama na Soji dake jihar Kaduna. Jirgin wanda ya sauka da sanyin safiya na dauke da jiragen yakin da gwamnatin Najeriya ta yi odarsu daga kasar Pakistan domin ci […]

WAEC za ta saki sakamakon jarrabawa ranar Laraba

WAEC za ta saki sakamakon jarrabawa ranar Laraba

Cibiyar shirya Jarrabawa ta Africa ta Yamma, wato WAEC, ta shirya tsaf  domin sakin sakamakon jarrabawar manyan makarantun sakandare na shekarar 2017, wato WASSCE, ranar Laraba, 19 ga watan Yuli. A wani bayani da cibiyar ta fitar ta fejinta na Facebook yayi nuni da cewar, daliban da suka rubuta jarrabawar WASSCE ta 2017 za su […]

An samu fashe-fashen bama-bamai a Maiduguri

An samu fashe-fashen bama-bamai a Maiduguri

Akalla mutane kusan goma sha daya (11) suka rasa rayukansu a was tagwayen fashewar abubuwa wadanda ake zargin bama-bamai ne, a ranar Talata da daddare a birnin Maiduguri. Wata majiya mai karfi ta tabbatar da cewar fashewar abun na farko da na biyu, ya faru ne daidai karfe 9.45 na dare a Mulaikalmari, kilomita shida […]

Babu sauran cin bashi ga Najeriya – Ministar Kudi

Babu sauran cin bashi ga Najeriya – Ministar Kudi

Ministar Kudi, Uwargida Kemi Adeosun, ta yi gargadi a ranar Talata cewar kada na Najeriya ta sake karambanin karbo bashi domin tafi da kasafin kudade, sai dai zai fi kyau ta yi amfani da hanyoyin samar da kudin shiga na cikin gida, domin tallafawa kasafin. Hakan yazo daidai lokacin da Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi osinbajo […]