Matata Da ‘Ya’yana 5 na Hannun Boko Haram

Wasu da iyalansu ke hannun mayakan Boko Haram na cigaba da bayyana halin damuwar da suke ciki, a dai dai lokacin da hukumomin Najeria ke ikirarin samun nasara a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Matata Da ‘Ya’yana 5 na Hannun Boko Haram

Editan BBC na Abuja, Naziru Mikailu ya yi kicibis da wani mutumin garin Bama dake jihar Borno, wanda yanzu yake Abuja, kuma wanda mayakan Boko Haram suka sace matarsa da ‘ya’yansa biyar, a cikin shekaru 4 da suka gabata. Ya dai nemi sakaya sunansa saboda matsalar tsaro. Ya fara da bayyana makasudin dalilin barin gidansa […]

Aisha ta gargadi Muhammadu Buhari

Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta gargadi mijinta cewa ba za ta goyi bayan takararsa a 2019 ba idan har al'amura suka ci gaba da tafiya a haka.

Aisha ta gargadi Muhammadu Buhari

A wata hira da ta musamman da BBC, ta ce gwamnatin mai gidanta ya yi watsi da fiye da rabin mutanen da suka yi mata wahala har ta samu mulki. “Bai gaya min cewa zai tsaya ko ba zai tsaya ba tukunna, amma na yanke shawara a matsayina na matarsa, cewa idan abubuwa suka ci […]