Gwamnatocin kasashen Arewacin Afrika na fargaban bazuwar mayakan ISIS a kasashensu

Yyinda kungiyar ISIS ke asarar yankunan da ta mamaye da a kasashen Syria da Iraq, kasashen Arewacin Afirka su na tsoron kada mayakan ISIS din su soma kwararawa zuwa yankinsu su tada hargitsi kamar yadda ake gani a Libya da Afghanistan

Gwamnatocin kasashen Arewacin Afrika na fargaban bazuwar mayakan ISIS a kasashensu

Yayin da kungiyar IS ta ke rasa mafi yawan yankunan da ke hannunta da kuma karfin ikonta a Syria da Iraqi, gwamnatocin kasashen yankin Arewacin Afirka, sun ce suna fargabar dawowar mayaka daga fagen yaki a Gabas ta Tsakiya, Ka iya haifar da rikici a yankunansu. “Yankin na fuskantar barazana… idan mayakan suka dawo,” inji […]

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Koma Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan da ya yada zango a birnin Landan daga Amurka, inda ya halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 a makon jiya.

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Koma Najeriya

Fadar shugaban kasar ce ta tabbatar wa BBC komawar shugaban gida. Sai dai ba ta yi karin haske ba game da abin da shugaban ya yi a Landan. Amma a baya shugaban ya fi zuwa can don duba lafiyarsa. Shugaban ya isa Landan ne ranar Alhamis daga birnin New York na Amurka. Kafin tafiyarsa, shugaban […]

Buhari Ya Bukaci Kawo Karshen Kisan Kare Dangi a Myanmar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su yi Allah-wadai da kisan kare dangin da sojojin Myanmar ke yi wa ‘yan kabilar Rohingya, akasarinsu Musulmi.

Buhari Ya Bukaci Kawo Karshen Kisan Kare Dangi a Myanmar

Buhari ya bukaci haka ne a yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 72 da aka fara gudanarwa a birnin New York na Amurka. Buhari ya alakanta rikicin jihar Rakhine ta Myanmar da kisan kare dangin da aka gani a Bosnia a shekarar 1995 da kuma Rwanda a shekarar 1994. Shugaba […]

Duba lafiyar Shugaba Buhari za a sake yi a London?

Fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari zai je London bayan ya kammala taron majalisar dinkin duniya da za a yi a Amurka makon gobe.

Duba lafiyar Shugaba Buhari za a sake yi a London?

Sanarwar da kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya aikewa manema labarai ta ce Shugaba Buhari zai je birnin New York na Amurka ranar Lahadi, domin halartar taron kwamitin koli na Majalisar Dinkin Duniya karo na 72, tare da sauran shugabannin kasashen duniya. A cewar sanarwar Shugaban “zai je birnin London a kan hanyarsa ta komawa […]

Ta yaya za a bambance mutuwa da dogon suma?

Baya ga kawar da zafin jiki, masu bincike na kokarin hana kwayoyin halitta mutuwa. "Za a yi ta gano muhimman al'amura a shekaru masu zuwa kan yadda sasan jiki ke da alakar rayuwa da mutuwa," acewar Abella.

Ta yaya za a bambance mutuwa da dogon suma?

A kashi na biyu, mun cigaba da duba yadda masana ilimin kiwon lafiya da kwararrun kimiyyar lafiya ke kara samun fahimtar yadda za a iya farfado da wadanda suke fama da ciwon bugun zuciya da kuma yadda za a iya ceto ran wadanda ake zaton su mutu bayan wani lokaci mai tsawo. Fahimtar at biyo […]