Kasashen Duniya Na Dabda Sanya Hannu Don Haramta Nukiliya

Kasashen duniya 51 sun shirya tsaf don sanya hannun kan wata yarjejeniya da za ta haramta mallakar makamin Nukiliya a duniya, abin da Amurka da sauran kasashen da suka mallaki irin wannan makamin ke matukar adawa da shi.

Kasashen Duniya Na Dabda Sanya Hannu Don Haramta Nukiliya

Wannan dai na zuwa ne a yayin da rikickin nukiliyar Koriya ta Arewa ke dada kamari, lura da yadda ta ke ci gaba da gwaje-gwajen makamin duk da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba ma ta. Kimanin kasashe 122 ne suka goyi bayan assasa dokar ta haramta mallakar makamin a wani taron Majalisar Dinkin […]

World Cup: Argentina Na Ci Gaba Da Fafutika

Argentina ta ci gaba da fafutikar ganin ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018 inda ta sha da kyar a hannun Venezuela, wacce ke mataki na karshe, da ci 1-1 a wasan da suka yi a gidan Argentinar.

World Cup: Argentina Na Ci Gaba Da Fafutika

Dan wasan Venezuela Jhon Murillo ya soma jefa kwallo a ragar Argentina ko da yake kwallon da suka ci kansu bayan komawa daga hutun rabin lokaci ta sa Argentina ta samu maki daya. Yanzu dai Argentina na matsayi na biyar a cikin kasashen da ke Kudancin Amurka kuma suna da sauran wasa biyu yayin da […]

Zakarun Nahiyoyi: Kamaru ta yi 1-1 da Australia

Zakarun Nahiyoyi: Kamaru ta yi 1-1 da Australia

Kamaru ta yi kunnen doki 1-1 da Australia a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha a ranar Alhamis din nan. Zakarun na Afirka su ne suka fara jefa kwallo a raga ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, ta hannun Zambo Anguissa. Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin ne kuma […]

Kofin Zakarun Nahiyoyi : Chile da Jamus sun yi 1-1

Kofin Zakarun Nahiyoyi : Chile da Jamus sun yi 1-1

Jamus da chile su ka tashi kunnen doki 1-1 a wasan cin kofin zakarun nahiyoyi da ake yi a Rasha a ranar Alhamis din nan. Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez shi ne ya ci wa Chile kwallonta minti shida da fara wasa bayan da Arturo Vidal na Bayern Munich, ya zura masa kwallon da dan […]