Kishin kasa ne ya sa na karbi mukamin minista — Okonjo- Iweala

Tsohuwar ministar kudi ta Nigeria, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce kishin kasa na daga cikin muhimman dalilan da suka sa ta rike mukamin ministar kudi har sau biyu a kasar.

Kishin kasa ne ya sa na karbi mukamin minista — Okonjo- Iweala

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana haka ne a wani shirin Turanci na rediyo da BBC ke gabatarwa mai suna “The Conversation” . Tsohuwar ministar ta ce, mahaifinta ya koyar da ita kishin kasa, dan haka ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta bayar da gudunmuwar da ta dace a lokacin da take rike da […]