Al-Bashir ya bukaci komawar wadanda suka tsere daga Darfur Daga Nura Ado Suleiman

Shugaban kasar Sudan, Omar Hassan al Bashir ya bukaci mazauna yankin Darfur da suka tsere daga gidajensu, su koma gida sakamakon kawo karshen yakin da aka gwabza wanda hallaka dubban mutane.

Al-Bashir ya bukaci komawar wadanda suka tsere daga Darfur Daga Nura Ado Suleiman

Akalla mutane sama da miliyan biyu da rabi ne suka tsere daga yankin na Darfur, sakamakon tashin hankalin da ya barke cikin shekara ta 2003, lokacin da ‘yan tawayen daga kananan kabilun yankin suka fara yakar sojojin kasar, bisa zargin kuntatawa yankin ta fannin siyasa da kuma tattalin arziki. Akasarin mutanen da suka tsere sun […]