Mayakan Saman Najeriya Sun Rugurguza Sabbin Sansanonin Boko Haram a Dajin Sambisa

Rarraba Dubi ra’ayoyi Jiragen leken asiri na sojojin yakin saman Najeriya sun gano wasu sabbin sansanoni da kungiyar Boko Haram ke ginawa a dajin Sambisa kuma sun rugurguzasu da lugudan wuta

Mayakan Saman Najeriya Sun Rugurguza Sabbin Sansanonin Boko Haram a Dajin Sambisa

Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar yace jiragen leken asirinsu sun gano yunkurin wasu mayakan Boko Haram na sake kafa sabbin sansanoni a dajin Sambisa. Sun gano wurare guda hudu da yan ta’addan ke akai, dalilin ma kenan da yasa suka kaddamar da shirin sintirin OPERATION RUWAN WUTA a wannan dajin. […]