Jam’iyyar PDP na baikon Atiku Abubakar

Jam’iyyar PDP na baikon Atiku Abubakar

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP reshen jihar Adamawa ta bayyana cewar zata tuntubi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar domin dawo dashi cikin jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar reshen na Adamawa Alhaji Abdulrahman Bobboi ya bayyana hakan a yayin da yake amsa tambayoyi ga ‘yan jarida a wajen wani taro a garin Yola dake jihar Adamawa. […]

Jam’iyyar APC ta Lashe Zabukan Jihar Legas

Jam’iyyar APC ta Lashe Zabukan Jihar Legas

Jam’iyyar mulki a Najeriya dama jihar Legas baki daya ta lashe ilahirin zabukan da aka gabatar na kananan hukumomi wanda akayi a ranar Asabar data gabata. Jaridar Punch ta ruwaito cewar jam’iyyar All Progressives Congress a lashe zabukan a kananan hukumomi 20 dake jihar Legas da kuma gundumomi 37 duka dai a cikin jihar. Sakamakon […]

Dan Arewa Na Farko Ya Tsaya Takarar Shugabancin Karamar Hukuma A Legas

A yayin da matasa a wasu sassan Najeirya ke ta kiraye kirayen raba kasa musanman tsakanin kudu maso gabashi da arewacin kasar, al’ummar kabilar yarbawa a jihar Legas sun amince da tsaida wani dan arewacin kasar a matsayin dan takarar mukamin shugaban karamar hukumar Agege.

Dan Arewa Na Farko Ya Tsaya Takarar Shugabancin Karamar Hukuma A Legas

WASHINGTON D.C — Shi dai wannan dan takara da jam’iyyar PDP ta tsayar a matsayin dan takarar shugabancin karamar hukumar Agege, mai suna Injiniya Auwal Tahir Maude, wanda aka fi sani da ATM, yana samun cikakken goyon baya daga ‘yan kabilar yarbawa. Da yake jawabi, dan takarar ya bayyana cewa daukacin ‘yan arewa mazauna wannan yanki […]

Lokaci Ya Yi Da PDP Za Ta Yi Sulhu a Tsakaninta – Sule Lamido

Masharhanta a Najeriya na ganin hukuncin da kotun koli ta yanke a Abuja, wanda ya bai wa bangaren Sanata Ahmed Makarfi hurumin shugabantar jam’iyar PDP, ka iya zama hanyar da jam’iyar za ta iya farfadowa daga doguwar suman da ta yi tun bayan da ta sha kaye a zaben 2015. Wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya zanta da tsohon gwamnan jihar Jigawa, AlhajI Sule Lamido, kan matakan da za su dauka domin daidaita jam'iyar.

Lokaci Ya Yi Da PDP Za Ta Yi Sulhu a Tsakaninta – Sule Lamido

WASHINGTON D.C. — Tsohon gwamnan jihar Jigawa a Najeriya, Alhaji Sule Lamido ya ce lokacin sulhu ya yi a tsakanin ‘ya’yan jam’iyar PDP mai adawa bayan hukuncin da kotu ta yanke a tsakiyar makon nan, wanda ya bayyana Sanata Ahmed Makarfi a matsayin halartaccen shugaban jam’iyar. “Wannan hukuncin ba wanda ya fadi babu wanda ya ji […]

PDP: ‘An tsawwala kudin fom din zabe a Kebbi’

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato PDP ta ce ba za ta iya shiga zabukan majalisun kananan hukumomi da za a yi a jihar Kebbi a yawancin wurare ba saboda karancin kudi.

PDP: ‘An tsawwala kudin fom din zabe a Kebbi’

Idan an jima dai ne za a bude rumfunan zabe domin zaben shugabannin da kansiloli na kananan hukumomin jihar 21. Jam’iyyar dai ta ce ta tsayar da ‘yan takarar shugabancin ne a kananan hukumomin shida kacal. Ibrahim Umar Ummai shi ne sakataren watsa labaran ta, Sakataren yada labaran jam’iyyar ya shaidawa BBC cewa hukumar zaben […]

PDP: Jonathan ya yi murna da nasarar Makarfi a kotun koli

PDP: Jonathan ya yi murna da nasarar Makarfi a kotun koli

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ya yi murna da nasarar da Sanata Ahmed Makarfi ya yi a kotun kolin kasar. “Ina taya jam’iyyata ta PDP murna saboda nasarar warware rikicin shugabanci da kotun kolin Najeriya ta yi”, in ji tsohon shugaban a shafinsa na Facebook da na Twitter. Ya yaba wa alkalan babbar kotun kasar, inda […]

Za a fatattaki miyagu daga gwamnatin Buhari — Aisha

Za a fatattaki miyagu daga gwamnatin Buhari — Aisha

Uwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta yi wani shagube kan al’amuran da suke faruwa a gwamnatin mijinta, tun bayan tafiyarsa jinya karo na biyu a birnin London. Ta wallafa shaguben ne a shafinta na Facebook ranar Litinin, inda ta yi amfani da abin da Sanata Shehu Sani na jihar Kaduna ya rubuta yana habaici […]

Jihar Jigawa Ta Gudanar Da Zabe Duk Da Kotu Ta Hana

Hukumar zaben jihar Jigawa ta gudanar da zabe a jihar Jigawa bayan kotu ta bada umarnin a dakatar da zaben.

Jihar Jigawa Ta Gudanar Da Zabe Duk Da Kotu Ta Hana

WASHINGTON DC — Yau hukumar zaben Jigawa ke gudanar da zaben shugabannin kanananan hukumomin jihar 27 da kuma kansiloli 284 a fadin jihar. Hukumar tace Jam’iyyu 10 ne ke fafatawa a zaben, amma Jam’iyyar PDP dake zaman babbar Jam’iyyar hamayya tace ba zata shiga zaben ba saboda girmama umarnin alkalin babbar kotun tarayya dake Dutse wanda […]

‘Rashin fita zaɓe na kassara shugabanci nagari’

‘Rashin fita zaɓe na kassara shugabanci nagari’

Yawan fitar jama’a ƙwansu da kwarkwatarsu su kaɗa ƙuri’u a lokacin zaɓuka, ka iya yin tasiri wajen tausasa gwiwar ‘yan siyasa su wanzar da shugabanci nagari. Jami’in wata ƙungiya mai sa ido kan zaɓuka, Assembly For Peace ne ya yi wannan ankaraswa jim kaɗan bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Jigawa da ke arewacin […]

PDP da APC duka abu guda ne – Ribadu

PDP da APC duka abu guda ne – Ribadu

Tsohon dan takarar shugabancin kasa a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu, ya ce babu wani bambanci tsakanin jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP a kasar. Sai dai tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin ta’annati (EFCC) ya ce da gaske gwamnatin Muhammadu Buhari take yi wurin yaki […]