Filato: Mutane 19 Sun Rasa Rayukansu a Wani Harin Ta’addanci Da Aka Kai

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane 19 a wani hari da wasu da ba a tantance ba suka kai a kauyen Ancha dake yankin Miango na karamar hukumar Basa.

Filato: Mutane 19 Sun Rasa Rayukansu a Wani Harin Ta’addanci Da Aka Kai

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato Peter Ogunyawo, ya shaidawa manema labarai cewa bakwai daga cikin wadanda aka kashen maza ne da mata shida da kananan yara shida, yayin da biyar din da suka sami raunuka ke karbar jinya a wani asibiti a Miango. Peter Ogunyawo, ya ce maharani da ake kyautata zaton fulani ne sun […]