Philippines: Mutane Sun Fara Fusata da Salon Yakar Miyagun Kwayoyi

Dubban mutane ne suka shiga wata zanga zangar da akayi a Manilla, babban birnin kasar Philippines, domin nuna rashin amincewa da yaki da masu safarar miyagun kwayoyin da shugaba Rodrigo Duterte ke yi, bayan kashe wani matashi.

Philippines: Mutane Sun Fara Fusata da Salon Yakar Miyagun Kwayoyi

A lokacin da akayi jana’izarsa ajiya, majiyoyi masu tushe sun rawaito cewa babu abinda ya hada matashin mai suna Leover Miranda, da mu’amala da miyagun kwayoyin. Mahaifin Miranda ya bukaci abi masa hakkin dan sa da aka kashe. A gefe guda kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce kashi biyu bisa uku na mutanen […]