An gano gidan ‘yan Boko Haram a Kano

Hukumomi a Najeriya sun ce sun gano wani gida a jihar Kano wanda suke zargin na 'yan kungiyar Boko Haram ne, bayan wani farmakin da jami'an tsaro suka kai ranar Asabar.

An gano gidan ‘yan Boko Haram a Kano

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Rabiu Yusuf, ya ce an kai samamen ne da misalin karfe biyu na dare bayan jami’ansu sun kama wasu mutum biyu a kan hanya da harsashin bindiga. Daga nan ne, sai ‘yan sanda suka je bincike gidan da mutanen suke zaune a Gayawa da ke karamar hukumar Ungogo. Ya ce […]