Musulman Rohingya na Fuskantar Wariya – Amnesty

Kungiyar kare hakkin dan'adam ta Amnesty International ta ce musulmai 'yan Rohingya a Myanmar na fuskantar wani nau'in wariya mai kama da ta launin fata karkashin jagorancin gwamnati.

Musulman Rohingya na Fuskantar Wariya – Amnesty

Rahoton baya-bayan nan na Amnesty ya bayyana kauyukan Rohingya a matsayin kurkukun talala, inda ya al’ummomin suka shafe gomman shekaru suna fuskantar musgunawa. Mai aikowa BBC rahoto daga Kudu maso Gabashin Asiya na cewa rahoton Kungiyar Amnesty daya ne daga cikin takardun da kungiyoyin kare hakkin dan’adam ke tattarawa da yiwuwar shigar da manyan hafsoshin […]

Mutanen Rohingya Ba ‘Yan Kasa Bane – Sojin Myanmar

Rundunar sojin Myanmar ta bukaci hadin-kan al’ummar kasar wajen bayyana wa duniya ainihin tushen ‘yan kabilar Rohingya.

Mutanen Rohingya Ba ‘Yan Kasa Bane – Sojin Myanmar

Rundunar ta ce, mutanen Rohingya ba su da asali a kasar, kuma tana kai mu su hari ne don kakkabe masu dauke makamai da ke cikinsu wadanda ta kira da ‘yan tawaye. Rundunar Sojin Myanmar ta bayyana cewa, tana kaddamar da hare-haren ne a yankin arewacin jihar Rakhine da zimmar kakkabe ‘yan tawayen na Rohingya […]

Shugabar Gwamnatin Myanmar Ta Musanta Kisan Musulmi

Daruruwan musulmai 'yan kabilar Rohingya ne a kowacce rana ke ci gaba da ficewa daga Myanmar zuwa makwabtaka don tsira da rayukansu bayan kisan kiyashin da ake ci gaba da yi musu a yankin Rakhine.

Shugabar Gwamnatin Myanmar Ta Musanta Kisan Musulmi

Karon farko tun bayan barkewar rikicin baya-bayan nan a Myanmar da ya hallaka Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da dama baya ga tilastawa daruruwa barin gidajensu, shugabar Gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta ce gwamnatin na kokarin kare hakkin kowanne bangare a Rakhine. Kalaman Aung San Suu Kyi na zuwa ne bayan kiran da MDD […]