Mutane sama da 345 ne suka rasa rayuka a girgizar kasa a Indonesia

Mutane sama da 345 ne suka rasa rayuka a girgizar kasa a Indonesia

Hukumomi a Indonesia sun bayyana cewar mutane sama da 345 ne suka rasa rayukan su a sanadiyar girgizar kasa da ta afku a yankin skakatawa na Lombok kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Antara ya ruwaito. Mafiya yawa sun rasa rayukan nasu ne a Kayangan dake arewacin tsuburin, kamar yadda Antara ta bayyana. Kusan mutane […]

Ana kwaso yaran da Boko Haram ta raba da Nigeria

An fara kwaso yaran da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, bayan sun tsere zuwa Jamhuriyar Kamaru, da nufin hada su da iyayensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Ana kwaso yaran da Boko Haram ta raba da Nigeria

Wasu daga cikin yaran dai marayu ne yayin da wasu kuma har yanzu iyayensu na nan da rai kuma an kwaso su ne cikin jirgin sama, wasu daga sansanin ‘yan gudun hijira na Minaoa. Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ce ta dauki gabarar wannan aiki na sada irin wadannan yara da iyaye ko […]

Wasu Mahajjata Tara Sun Isa Madina a Keke Daga London

Wasu mahajjatan Birtaniya su tara sun isa birnin Madinah na Saudiyya a keke, bayan sun yi tafiyar kilomita 3,000 daga London.

Wasu Mahajjata Tara Sun Isa Madina a Keke Daga London

Hukumomin Saudiyya sun tarbi mutanen a Madina cike da murna da jinjina a gare su. Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito cewa kungioyin masu tseren kekuna na Madinah da Taibah ne suka tarbi mahajjatan karkashin jagorancin hukumar wasanni ta Saudiyya, inda aka dinga yi musu kade-kade da watsa musu furanni don […]

Mutane 312 sun mutu a ambaliyar Saliyo

Akalla mutane 312 ne suka rasa rayukansu, in da sama da dubu 2 suka rasa gidajensu sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa a babban birnin Freetown na Saliyo a yau Litinin.

Mutane 312 sun mutu a ambaliyar Saliyo

Rahotanni na cewa, dakunan ajiye gawarwaki sun cika makil, kuma jama’a na ci gaba da neman ‘yan uwansu da makusantansu. Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ce, ya shaida yadda aka yi ta kwashe gawarwakin mutane da kuma yadda gidaje suka nutse a ruwa musamman a wasu yankuna biyu na birnin, in da […]

Gobara ta hallaka rayuka a Anambra

Ana samun alkaluma masu cin karo da juna na adadin mutanen da suka rasu sakamakon gobara a wata masana'antar iskar gas a garin Nnewi na jihar Anambra.

Gobara ta hallaka rayuka a Anambra

Hukumomin ‘yan sanda wadanda suka tabbatar da aukuwar gobarar, ba su yi karin haske ba dangane da adadin mutanen da suka kone ba. Hukumar agaji ta NEMA ta ce mutane biyar ne suka rasu a yayin da mutane bakwai suka samu raunuka. NEMA ta ce gidaje shida da motoci 22 ne suka kone sakamakon gobarar. […]

Gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijirar Syria

Gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijirar Syria

Akalla mutum daya ne ya mutu bayan wata gobara da ta tashi a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke tsaunin Bekaa da ke gabashin Lebanon. Rahotanni farko sun ce mutum uku ne suka mutu sanadiyyar gobarar. Al’amarin ya faru ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke kusa da garin Qab Elias a tsaunin […]

Kamfanin sufuri na Uber ya mayar wa fasinjoji kudade

Kamfanin sufuri na Uber ya mayar wa fasinjoji kudade

Kamfanin Uber ya mayar wa fasinjojin da suka yi amfani da manhajar kamfanin a kusa da gadar da aka kai harin ta’addanci na birnin Landan. Kamfanin sufurin ya sha suka daga jama’a a zaurukan zumunta na intanet saboda kyale kudin mota ya tashi a lokacin harin wanda aka kai da misalin karfe 10 na dare. […]