An Zargi ‘Yan Rohingya Da Kashe ‘Yan Hindu

Rundunar sojan Bama ta zargi Musulmi 'yan ta-da-kayar-baya na Rohingya da kashe mace 20 da namiji takwas har ma da yara, wadanda ta ce ta gano gawawwakinsu a wani makeken kabari.

An Zargi ‘Yan Rohingya Da Kashe ‘Yan Hindu

Sojojin sun ce gawawwakin da suka gano na ‘yan Hindu ne, wadanda dubbansu ke cewa ‘yan ta-da-kayar-bayan sun tilasta musu tserewa daga kauyukansu. Ba a dai iya tantance sahihancin wannan bayani na rundunar sojan Myanmar ba. Musulmai ‘yan Rohingya dubu 430 ne suka gudu daga Myanmar zuwa Bangladesh, sakamakon hare-haren da sojoji ke kai wa […]

Kisan Musulmin Rohingya ya yi kama da kisan kiyashin Rwanda – Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nemi Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta dauki mataki kan musgunawar da ake yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Kisan Musulmin Rohingya ya yi kama da kisan kiyashin Rwanda – Buhari

A jawabin da ya gabatar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 72, Shugaba Buhari, ya ce irin abun da yake faruwa a Myanmar ya yi kama da irin kisan kiyashin da ya aka yi Bosniya a shekarar 1995 da kuma Rwanda a shekarar 1994. Mutane a sassan duniya sun yi ta Allah-wadai kan irin […]

‘Yan Ghana Sun Yi Zanga-Zanga Kan Musgunawa Musulman Rohingya

Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda ake musguna wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a Myanmar

‘Yan Ghana Sun Yi Zanga-Zanga Kan Musgunawa Musulman Rohingya

Wasu daruruwan Musulmai a birnin Accra na kasar Ghana sun gudanar da wata kasaitaciyar zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu da cin zarafin da suka ce ake yi wa Musulmai ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar. Masu zanga-zangar sun kuma nuna rashin jin dadinsu game da abun da suka kira ci gaba da sayar wa […]

Gwamnatin Bangladesh zata takaita zirga-zirgar ‘yan gudun hijirar Rohingya

Gwamnatin Bangladesh zata takaita zirga-zirgar ‘yan gudun hijirar Rohingya

Bangladesh ta ce, zata takaita zirga-zirgar ‘yan gudun hijira na kabilar Rohingya da suke shigo mata, bayan tserewa daga Myanmar. ‘Yan sandan kasar sun ce tilas ne ‘yan gudun hijirar na Kabilar Rohingya, su zauna a sansanonin wucin gadin da gwamnati ta basu a maimakon fantsama cikin kasar. Gwamnatin Bangladesh ta kuma sanar da shirinta […]

Musulman Rohingya Dubu 60 Sun Nemi Mafaka a Bangladesh

Tuni dai Hukumar bada tallafin abinci ta duniya ta dakatar da bada tallafin abincin ga jihar ta Rakhine mai fama da rikicin.

Musulman Rohingya Dubu 60 Sun Nemi Mafaka a Bangladesh

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, akalla Musulman Rohingya dubu 60 ne suka tsere zuwa Bangladesh a cikin kwanaki takwas sakamakon rikicin da ake fama da shi a jihar Rakhine da ke Myanmar. Mai magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Vivian Tan ta shaida wa kamfanin Dillancin labaran Faransa na […]

Shugabar Gwamnatin Myanmar Ta Musanta Kisan Musulmi

Daruruwan musulmai 'yan kabilar Rohingya ne a kowacce rana ke ci gaba da ficewa daga Myanmar zuwa makwabtaka don tsira da rayukansu bayan kisan kiyashin da ake ci gaba da yi musu a yankin Rakhine.

Shugabar Gwamnatin Myanmar Ta Musanta Kisan Musulmi

Karon farko tun bayan barkewar rikicin baya-bayan nan a Myanmar da ya hallaka Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da dama baya ga tilastawa daruruwa barin gidajensu, shugabar Gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi ta ce gwamnatin na kokarin kare hakkin kowanne bangare a Rakhine. Kalaman Aung San Suu Kyi na zuwa ne bayan kiran da MDD […]

Rikici ya Tilastawa ‘Yan Rohingya 90,000 Tserewa Zuwa Bangladesh

Wasu 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikici yayinda suka tafiya cikin tabo a kan iyakar Myanmar da Bangladesh, ranar 1 ga Satumban 2017.

Rikici ya Tilastawa ‘Yan Rohingya 90,000 Tserewa Zuwa Bangladesh

Hukumomin agaji sun yi gargadin cewa Sansanonin ‘yan gudun hijira a kasar Bangladesh zai iya fuskantar tarin matsaloli saboda yawan jama’ar da ke cikinsa, tun bayan karuwar dubban Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da ke ci gaba da tururuwa cikinsa don gujewa rikicin Myanmar. Majalisar Dinkin Duniya tace ‘yan kabilar ta Rohingya akalla dubu 90,000 ne […]

Myanmar ‘Yan Kabilar Rohingya 37,000 Sun Tsere Cikin Awanni 24’

'Yan kabilar Rohingya mafi akasarinsu Musulmi, suna turereniyar samun abinci, bayanda suka tsere zuwa Bangladesh.

Myanmar ‘Yan Kabilar Rohingya 37,000 Sun Tsere Cikin Awanni 24’

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla ‘yan Kabilar Rohingya mafi akasarinsu Musulmi dubu talatin da bakwai ne, (37,000) suka tsere zuwa kasar Bangladesh cikin awanni 24, lamarin da ta bayyana shi a matsayin gudun hijira mafi girma da aka taba gani cikin karamin lokaci tun bayan sabon tashin hankalin da ya barke a kasar Myanmar. […]