Al’ummar Arewa Maso Gabas Sun Gudanar da Taro Kan Sake Fasalin Najeriya

A cigaba da muhawara kan sake fasalin Najeriya al'ummar arewa maso gabashin Najeriya sun yi taro a Bauchi inda suka tattauna suka bada tasu shawarar kan yadda ya kamata Najeriya ta kasance.

Al’ummar Arewa Maso Gabas Sun Gudanar da Taro Kan Sake Fasalin Najeriya

Mahalarta taron sun hada da ‘yan siyasa, iyayen kasa, kungiyoyin kare hakkin ‘yan kasa, kungiyoyin mata da matasa da dai sauransu. Taron ya gayyato mutanen da suka yi magana kan sallon mulki, sabon lale da tsarin fitar da sabon mulki da irin hukuncin da ya kamata a aiwatar kan masu yiwa mata fyade da masu […]