Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?

Wasu mata sun gudanar da zanga-zanga kan yadda al'umma a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ke yin wasarairai da matsalar karuwar fyade.

Me ya sa mutane ba sa nuna damuwa kan karuwar fyade a Kano?

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Hajiya Aisha Dan kani ta ce sun gudanar da zanga-zangar ce don zaburas da jama’a kan alhakin da ya rataya a wuyansu na shawo kan karuwar fyade. Zanga-zangar wadda tsoffin daliban makarantar St. Louis suka shirya amma gwamnatin jihar Kano ta ce kada a yi, ta ci gaba da gudana […]