‘Sojoji Sun Kai Samame Gidan Jagoran Biafra’

A kalla mutum 22 ne suka rasa rayukansu lokacin da rudunar Sojin Najeriya ta kai samame gidan madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu a jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya, kamar yadda dan uwansa ya shaida wa BBC.

‘Sojoji Sun Kai Samame Gidan Jagoran Biafra’

“Sojoji sun isa gidanmu dauke da makamai da ayarin motoci kirar Hilux kimanin guda 20. Sun bude wa jama’a wuta a gidan wanda hakan ya sa kimanin mutum 22 sun rasa rayukansu,” in ji Prince Emmanuel Kanu. Har ila yau, ya yi zargin cewa sojojin sun lalata fadar mahaifinsu wanda basaraken gargajiya ne a yankin. […]