Kotu ta yi watsi da karar ‘yan Shi’a

Wata Kotun tarraya a jihar Kadunan Najeriya ta yi watsi da karar da jagoran kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya shigar kan sojin kasar.

Kotu ta yi watsi da karar ‘yan Shi’a

Zakzaky ya shigar da karar ne domin neman diyya bayan soji sun kashe daruruwan mabiyansa tare da lalace kadarorinsa a watan Disambar shekarar 2015. Sai dai alkalin kotun, Mai Shari’a Salisu Sha’aibu, ya ce kotun ta yi wasti da karar ne saboda ba ta gamsu da hujjojin da masu gabatar da kara suka shigar ba. […]

Saudiyya ta daƙile kai hari Masallacin Ka’aba

Saudiyya ta daƙile kai hari Masallacin Ka’aba

Ƙasar Saudiyya ta ce ta daƙile wani “yunƙurin harin ta’addanci” da aka so kai wa Masallacin Harami a Makkah – wurin ibada mafi tsarki ga Musulmi. Wani ɗan ƙunar-bakin-wake ya tarwatsa kansa lokacin da dakarun tsaro suka zagaye ginin da yake ciki, in ji ma’aikatar harkokin cikin gida. Ginin ya ruguje, inda ya jikkata mutum […]