Za a Kai Gwamnatin Taraba kotun ICC

Za a Kai Gwamnatin Taraba kotun ICC

  Wani babban Laura Farfesa Yusuf Dankofa tare da kungiyar Miyatti Allah sun bayyana cewar za su maka Gwamnatin Taraba a kotun hukunta laifukan yaki ta duniya bisa zargin hannu a kisan kiyashi da aka yi wa fulani a Mambila dake jihar. A wata hira da yayi da sashen Hausa BBC, Farfesa Yusuf Dankofa yace […]

Tawagar Sanata Musa Kwankwaso Ta Kai Ziyara Tsaunin Mambila

Rashin ayyukan yi, ilimi da shaye shaye tsakanin matasa na daga cikin dalilai da suke haddasa tashe tashen hankula da suka abku a yankin tsaunin Mambila na karamar hukumar Sardsauna dake jihar Taraba.

Tawagar Sanata Musa Kwankwaso Ta Kai Ziyara Tsaunin Mambila

Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar tarayya ta Kano ta tsakiya a Sanata Musa Kwankwaso yana mai cewa matasan da basu da aikin yi ne ake anfani dasu wajen haddasa tashe tashen hankali. Ya furta haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar mazabarsa ziyarar jajantawa da ban hakuri ga mazauna yankin da ke da Hausawa […]

“An yi wa Fulani kisan-ƙare-dangi a Taraba”

“An yi wa Fulani kisan-ƙare-dangi a Taraba”

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kashe-kashen da aka yi wa Fulani a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar a matsayin kisan-kare-dangi. Babban kwamandan runduna ta uku ta sojan kasar da ke Jos, wanda ya bayyana hakan, ya dora alhakin hakan kan shugabannin kabilar Mambila. Birgediya Janar Benjamin Ahanotu ya fadi hakan ne a […]

An tura ƙarin jami’an tsaro jihar Taraba

An tura ƙarin jami’an tsaro jihar Taraba

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ba da umarnin aikewa da karin jami’an tsaro wasu garuruwa da kauyukan jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya. A farkon makon nan ne wani sabon rikici ya sake barkewa tsakanin Fulani da ‘yan kabilar Mambila a karamar hukumar Sardauna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. A […]

Gwamnatin Tarayya Tayi Taron Gaggawa Kan Rikicin Mambilla A Jahar Taraba.

Hafizu Ibrahim hadimin mukaddashin shugaban kasa ne ya bayyana haka, bayan zaman da aka yi kan wannan batu.

Gwamnatin Tarayya Tayi Taron Gaggawa Kan Rikicin Mambilla A Jahar Taraba.

WASHINGTON DC — Mukaddashin shugaban Najeriya Parfessa Yemi Osinbajo, ya kafa kwamitin bincike kan rikicin Taraba. Parfessa Osinbajo, yayi ta’aziyya ga iyalan wadanda wannan rikici na tsaunin Mambilla ya shafa. Babban hadimin mukaddashin shugaban kasa Hamisu Ibrahim, wanda ya bayyana haka, yace Parfessa Osibanjo, ya gana ne da shugabannin hukumomin tsaro tareda Gwamnan jahar Darius Isiyaku, […]

Sarakuna A Taraba Sun Yi Kiran A Samu Zaman Lafiya A Yankin Gembu

Biyo bayan irin yawan kashe kashen da suka auku a yankin Gembun jihar Taraba musamman tsakanin manoma da makiyaya sarakunan yankin sun gargadi al'ummominsu da su rungumi zaman lafiya, suyi watsi da makamansu su kuma kiyaye yin kalamun da ka harzuka mutane

Sarakuna A Taraba Sun Yi Kiran A Samu Zaman Lafiya A Yankin Gembu

WASHINGTON DC — Shugabannin gargajiya na yankin Gembu dake jihar Taraba da ya yi fama da tashe-tashen hankula da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin jama’a sun yi kira a kai zuciya nesa don samun dawamammiyar zaman lafiya. Sarkin Mambila Dokta Shehu Audu Baju na biyu ya furta haka lokacin da yake jawabi a fadarsa […]