Saudi Arabia: An Kama Yaron Da Ya Yi Rawar ‘Macarena’

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama wani yaro mai shekara 14 wanda aka nuna a wani bidiyo yana taka rawar wakar 'Macarena' a kan titi.

Saudi Arabia: An Kama Yaron Da Ya Yi Rawar ‘Macarena’

Bidiyon ya ja hankulan dubban mutane a Twitter. Hukumomi na yi wa yaron tambayoyi bayan an zarge shi da “nuna rashin tarbiyya” a birnin Jeddah, in ji wata sanarwa. Ba a tabbatar da ko yaron dan kasar ta Saudiyya ne ba, kuma ko hukuma za ta gurfanar da shi a kotu. A farkon wannan watan […]

Trump Ya Caccaki Masu Sukar Shi

Cikin fushi shugaba Donald Trump na Amurka ya ci gaba da amfani da hanyar sadarwan nan da ya saba amfani da ita wato Twitter, domin caccakar wadanda yake kallo a matsayin makiyansa, ciki harda daya daga cikin ‘yan majalisar zartarwarsa wato atoni janar na Amurka.

Trump Ya Caccaki Masu Sukar Shi

Matakin daya jawo suka daga shugabanin jam’iyar Republican da kuma kafofin yada labaru masu ra’ayin rikau wadanda galibi suke goyon ga shugaban Kwana daya baya shugaba Trump ya bayyana Atoni janar din a matsayin wanda baida wani karfin gwiwa a gare shi. Sakonin da shugaban yasa dandalin tweeter, ko tantama babu, suna nuni da cewa […]

An kai karar Trump kan hana wasu shiga Twitter

A shekara 30 da ta wuce an kai shugaban kasar Amurka Donald Trump kara kotu sau 4,000.

An kai karar Trump kan hana wasu shiga Twitter

Yanzu an kara kai shi kotu bayan da wasu mutum bakwai sun kai kararsa sakamakon toshe su da ya yi daga tofa albarkacin bakinsu a shafinsa na Twitter. Mr Trump yana amfani da Twitter sosai wajen yabon masoyansa da kuma mayar da martani ga masu sukarsa. Wata cibiya mai goyon bayan ‘yancin fadin albarkacin baki […]

An kai tsegumin Sarauniyar Ingila wajen ‘yan sanda

An kai tsegumin Sarauniyar Ingila wajen ‘yan sanda

An kai rahoton Sarauniyar Ingila ga ‘Yan sandan West Yorkshire saboda rashin sanya maɗauri a cikin motar masarauta a kan hanyarta ta zuwa bikin buɗe zaman Majalisa. Wani mutum ne ya buga lambar kar-ta-kwana ta 999, inda ya tsegunta wa ‘yan sanda cewa Sarauniya ba ta sa bel ba a motar da ake tuƙa ta […]