Boko Haram ta bullo da sabon salon harin kunar bakin wake

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta gargadi jama'a game da sabon salon da kungiyar Boko Haram ta bullo da shi wajen kai hare-haren kunar bakin wake kan gine-ginen gwamnati.

Boko Haram ta bullo da sabon salon harin kunar bakin wake

Mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan jihar, Victor Isuku ya shaida wa BBC cewa kananan yaran na kiwo ne a wani daji lokacin da ‘yan Boko Haram din suka daura musu damarar bama-baman tare da gargadinsu kada su kwance har sai sun isa gida. Ya kuma kara da cewa, ”An daura wa Gambo Bukar […]