Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?

Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?

Rawar da Farfesa Yemi Osinbajo yake takawa a matsayin mukaddashin shugaban kasa sakamakon rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya shafe watanni a wajen kasar na ci gaba da jan hankalin jama’a. Yayin da wasu ke cewa yana taka rawar gani, wasu kuwa cewa suke yi yana dari-dari. Rashin lafiyar shugaban, wanda ba a bayyana […]

Osinbajo zai rantsar da sabbin ministoci 2 ranar Laraba

Osinbajo zai rantsar da sabbin ministoci 2 ranar Laraba

Mukaddashin Shugaban Nigeria Yemi Osinbajo zai rantsar da sabbin ministocin nan biyu da suka kwashe fiye da wata biyu suna dakon shan rantsuwar da safiyar Larabar nan. A wani sakon a shafinsa na twitter, Mataimakinsa kan Watsa Labarai Laolu Akande ya ce za a rantsar da su ne a farkon taron majalisar ministocin kasar na […]

Buhari ya gana da wasu gwamnoni a London

Buhari ya gana da wasu gwamnoni a London

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu gwamnonin kasar a birnin Landan na kasar Birtaniya. Shugaban wanda yake ci gaba da jinya ya gana ne da gwamnonin jam’iyyar APC da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana. Tawagar da ta kai masa ziyara ta kunshi gwamnonin jihohin Kaduna da Nasarawa da […]

Buhari ya yi waya da tsohon shugaban APC Bisi Akande

Buhari ya yi waya da tsohon shugaban APC Bisi Akande

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasar Cif Bisi Akande wayar tarho. Shugaba Buhari, wanda ya kwashe sama da wata biyu yana jinya a birnin London, ya yi wa Cif Akande ta’aziyya bisa ga rasuwar matarsa Madam Omowunmi Akande. Wata sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar […]

‘Muna sa ran dawowar Buhari nan ba da jimawa ba’

‘Muna sa ran dawowar Buhari nan ba da jimawa ba’

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce nan ba da jimawa ba shugaba Buhari zai dawo daga London inda ya je jinyar rashin lafiya. Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan ne ga manema labarai a fadar gwamnatin kasar a ranar Laraba, gabannin taron majalisar ministocin kasar. Mukaddashin shugaban kasar ya kuma ce shugaba Buharin yana […]

Osinbajo na shirin yin girgiza a Majalisar Zartarwa

Osinbajo na shirin yin girgiza a Majalisar Zartarwa

  Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya kammala dukkan shirye-shirye domin yin girgiza a Majalisar zartarwa ta kasa. Bayanan da suka fito daga wata majiya kumaJaridar The Nation ta ruwaito, ya nuna cewar faruwar na kadan daga cikin tattaunawar da Mukkadashin Shugaban Kasa yayi tsakaninsa da Shugaba Buhari lokacin da ya kai masa ziyara ranar […]

Babu sauran cin bashi ga Najeriya – Ministar Kudi

Babu sauran cin bashi ga Najeriya – Ministar Kudi

Ministar Kudi, Uwargida Kemi Adeosun, ta yi gargadi a ranar Talata cewar kada na Najeriya ta sake karambanin karbo bashi domin tafi da kasafin kudade, sai dai zai fi kyau ta yi amfani da hanyoyin samar da kudin shiga na cikin gida, domin tallafawa kasafin. Hakan yazo daidai lokacin da Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi osinbajo […]

Yemi Osinbajo ya yi ‘kyakkyawar’ ganawa da Buhari

Yemi Osinbajo ya yi ‘kyakkyawar’ ganawa da Buhari

Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a birnin London wanda ya kwashe fiye da wata biyu yana jinya a can. Wata sanarwa da kakakin farfesa Osinbajo, Laolu Akande ya wallafa a shafinsa na Twitter, a daren Talata, ta ce “Nan ba da jimawa ba za mu sanar da jama’a […]

Takaddama Ta Kunno Kai A Majalisar Dattawan Najeriya

Takkadama da ta kunno kai ta yunkurin dakushe hurumin mukadashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ja rarrabuwar kawuna a Majalisar Dattawa.

Takaddama Ta Kunno Kai A Majalisar Dattawan Najeriya

WASHINGTON DC — A wani zama da majalisar ta yi da hakkan ya fito fili karara Sanata Ahmad Sani Yerima, ya ce miko sunan da Farfesa Yemi Osinbajo yayi ya kara tabbatar da cewa lallai majalisar tana da cikakken iko kenen. Wannan alamari ya harzuka Sanata Abaribe, da ya nemi ya nuna cewa shugaban majalisar dattawa […]

Majalisa Ta Gindayawa Bangaren Zartaswa Sharudda Kafin Ta Tantance Jami’anta

Majalisar Dattawan Najeriya ta jaddada matsayinta na cewa ba za ta sake tantance sunan kowa da Fadar shugaban kasa za ta gabatar ba har sai ta cika wasu sharudda da suka hada da amincewa da cewa ita ke da hurumin tantance jami'an da za a nada a mukamai.

Majalisa Ta Gindayawa Bangaren Zartaswa Sharudda Kafin Ta Tantance Jami’anta

Majalisar wacce ta nuna rashin jin dadinta kan kin cire Ibrahim Magu duk da cewa ta taki tabbatar mai da mukaminsa, a baya-bayan nan ta ki tantance Mr Lanre Gbajabiamila da bangaren zartaswar ya mika mata. Daga cikin sharuddan da majalisar akwai batun sai mukaddashin Shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo ya amince cewa majalisar na […]