Me ya sa shugabannin Afirka ke zuwa kasahen ketare jinya?

Shugabannin kasashen Najeriya da Angola da Zimbabwe da Benin, da Algeria na da abubuwan da suke kamanceceniya, wato rashin yarda da tsarin kiwon lafiyar kasashensu.

Me ya sa shugabannin Afirka ke zuwa kasahen ketare jinya?

Ta fuskar lokutan da suka shafe suna jinya a kasar waje, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari mai shekara 74, shi ne na farko a cikinsu, amma a shekarun da suka gabata dukkan wadannan shugabannin sun ketara wasu kasashen don duba lafiyarsu. A lokuta da dama suna tafiya su bar asibitoci ba isasshen kudin da za […]

Bankuna a Zimbabwe za su fara karbi dabbobi a jingina

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya saka hannu kan wata sabuwar doka da za ta ba kananan masana'antu da 'yan kasuwa damar su bayar da dabbobi da wasu kayan amfani a gida a zaman jingina wajen samun bashi.

Bankuna a Zimbabwe za su fara karbi dabbobi a jingina

Hukumomin kasar dai sun ce an kafa dokar ne domin shawo matsalar rashin jari da kananan masana’antu ke fuskanta sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. Wannan dokar ta bai wa bankuna kasuwanci a Zimbabwe damar su karbi dabbobi kamar shanu, da awaki, da kuma tumaki a zaman jingina wajen bayar da rancen kudi. […]

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya yi hatsarin mota a Harare

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe ya yi hatsarin mota a Harare

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya yi hatsarin mota yayin da yake barin filin jirgin saman birnin Harare bayan ya dawo daga tafiya. Ko da yake, shugaban bai ji rauni ba, amma mai dakinsa Grace wadda suke tare a mota ta jikkata. Shugaban ya sauka a filin jirgin saman ne yayin da ya dawo jinya […]