Tarayyar Turai Taci Tarar Google $2.7

Hukumin kungiyar tarayyar Turai ta dankarawa kamfanin Google tara ta kimanin dalar Amurka biliyan biyu da miliyan dari bakwai a sakamakon wani cin amana da aka sami kamfanin dashi wanda kuma shine karo na farko da aka taba yiwa wani kamfani a Amurka irinsa mafi girma.

Tarayyar Turai din tace ta samu Google da laifin hana masu neman yin sayayya a shafin ta na gizo gizo da samun irin abinda suke bukata wanda hakan kan sa Google tilastawa mutane sayan nasu kayan.

Hukumin sunce tilas ne kamfanin na Google ya sauya tsarin tafiyar sa a cikin kwanaki casa’in ko kuma ya sake fuskantar wata sabuwar tarar.

Mai magana da yawun kungiya, Margrethe Vestager tace abinda Google tayi ba dai dai bane a bisa tsarin tarayyar turai na cin amanar yanar gizo gizo inda takan hana wadan su kamfanonin samun damar damawa a wannan fanni.

A nata bangaren, kamfanin Google tace a wata sanarwa cewar tana iya bakin kokarin ta don ganin ta nuna tallace tallace da zasu amfani masu saya da kuma sayarwa.

588total visits,1visits today


Karanta:  Kamfanin sufuri na Uber ya mayar wa fasinjoji kudade

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.