Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

A Najeriya sojojin kasar da dama na jibge a wasu yankuna domin gudanar da sintiri da atisaye, musamman domin kwantar da hankulan jama'a da kuma wanzar da zaman lafiya. Shin mene ne tasirin irin wannan sintiri?

A sassa daban daban na Najeriya dakarun kasar kan gudanar da atisaye na musamman inda akan jibge su su yi kwana da kwanaki ko kuma su dauki wani tsawon lokaci suna atisayen.

Akan kai dakarun ne yankunan da ke fama da wasu matsaloli na musamman, misali a yankin da ake fama da matsalar satar shanu ko tsagerun yankin Niger Delta ko masu fashi da makami ko satar mutane.

Sannan akan shirya irin wannan atisaye har ila yau a yankunan da ake fama da matsanancin rashin tsaro kamar na Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, da kuma matsalar ‘yan aware ta ‘yan kungiyar IPOB da ke kudu maso gabashin kasar.

Har ila yau akan aike da dakaru, saboda yankunan da ke fama da rikicin kabilanci ko na addini.

Daga cikin ire-iren wadannan sintiri, akwai “Operation Lafiya Dole” da “Operation Crack Down” da “Operatino Gama Aiki” da “Operation Safe Corridor” da “Operation Safe Haven” da “Operation Sharar Daji” da “Operation A Watse” da dai sauransu. Amma shin wanne irin tasiri ire-iren wadannan sintiri ke yi a sassan Najeriya, ku saurari rahoton Hassan Maina Kaina:

Asalin Labari:

VOA Hausa

1106total visits,2visits today


Karanta:  Cutar da ba a Sani ba ta Kashe Mutum 62 a Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.