Trump Ya Caccaki Masu Sukar Shi

Cikin fushi shugaba Donald Trump na Amurka ya ci gaba da amfani da hanyar sadarwan nan da ya saba amfani da ita wato Twitter, domin caccakar wadanda yake kallo a matsayin makiyansa, ciki harda daya daga cikin ‘yan majalisar zartarwarsa wato atoni janar na Amurka.

Matakin daya jawo suka daga shugabanin jam’iyar Republican da kuma kafofin yada labaru masu ra’ayin rikau wadanda galibi suke goyon ga shugaban

Kwana daya baya shugaba Trump ya bayyana Atoni janar din a matsayin wanda baida wani karfin gwiwa a gare shi. Sakonin da shugaban yasa dandalin tweeter, ko tantama babu, suna nuni da cewa yana son Session yayi murabus.

Yau dai sama da wata guda Ke nan Trump ya fada ya sake nanatawa ya bayyana rashin hankurin sa akan yadda ake samun tafiyar hawainiya game da binciken da ake yi, amma kuma kusan kullun batun alakar kanfen dinsa da kasar Ruasha shine labaran da ke fitowa a shafukar jaridu.

Wannan sakon nasa ta twitter na wannan karon ga bisa dukkan alamu ya dauki sabon salo domin ko ya kudiri aniyar ganin sai ya kunyatar da Jeff Session minister shari’ar sa.

Asalin Labari:

VOA Hausa

510total visits,1visits today


Karanta:  Rasha ta Bukaci Amurka Data Dawo Mata da Gidajen Ta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.