An tura ƙarin jami’an tsaro jihar Taraba

Yemi Osinbajo

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ba da umarnin aikewa da karin jami’an tsaro wasu garuruwa da kauyukan jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya.

A farkon makon nan ne wani sabon rikici ya sake barkewa tsakanin Fulani da ‘yan kabilar Mambila a karamar hukumar Sardauna, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

A ranar Alhamis ne mukaddashin shugaban ya yi wani taron gaggawa da Gwamnan Jihar ta Taraba Darius Dickson Ishaku, da kuma manyan hafsoshin tsaron kasar kan yadda rikicin ya ke kara kamari.

Har ila yau, Farfesa Osinbajo ya yi Allah-wadai da masu tada zaune tsaye, inda ya ce za a hukunta duk wadanda aka samu da laifi.

Mista Osinbajo ya ba da umarnin aika wa da bataliya daya ta sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wuraren da rikicin ya shafa.

Asalin Labari:

BBC Hausa

935total visits,1visits today


Karanta:  Majalisa Ta Gindayawa Bangaren Zartaswa Sharudda Kafin Ta Tantance Jami'anta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.