Wanene sabon yariman Saudi Arabia?

Tun da mahifinsa ya zama sarkin Saudiyya, tauraruwar Yarima Mohammed ke haskawa – kuma a yanzu yana dab da zama sarki.

Saboda ya cimma burinsa, matashin dan sarkin ya rika samun karin mukami akai-akai, wannan ya sa an rika ture wasu ‘yan gidan sarautar a gefe.

Ga abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya.

Ya tattara ikon don amfanin gidansu

Dangantakar yarima mai jiran gado da mahifinsa ta kut-da-kut ce tun gabannin zaman mahaifinsa sarki.

A lokacin yana gwamnan Riyadh a shekarar 2009, sarkin ya nada Yarima Mohammed a matsayin babban mai ba shi shawara.

Duk da cewa ba a saba ganin irin hakan ba a kasar ta Saudiyya.

Mafi muhimmancin batu a rayuwar siyasarsa ya faru ne a watan Afrilun 2015, yayin da sarkin na Saudiyya ya nada wadanda zasu gaje shi.

A lokacin an nada Mohammed bin Nayef a matsayin yarima mai jiran gado, wanda wannan yasa ya maye gurbin dan uwan sarkin Muqrin bin Abdul Aziz.

Amma abun lura shi ne sarkin ya nada yarima Mohammedyi a matsayin mataimakin yarima mai jiran gado.

Wadannan sauye-sauyen ne suka buda masa hanyar gadon mahaifin nasa da aka raba bin Nayef da mukaminsa.

Sabon yariman shi ne mataimakin firai minista, kuma ministan tsaron kasar.

Mai son karfafa tsaro ne

Bayan da Salman bin Abdulaziz ya zama sarki a watan Janairun 2015, yayi wasu sauye-sauyen da suka bai wa dan nasa damar gadonsa.

Ya kasance ministan tsaro mafi karancin shekaru a duniya – a yayin da aka nada shi yana da shekara 29 ne.

Bayan nada shi da wata biyu ne gamayyar kasashen da Saudiyyar take jagoranta suka kaddamar da yaki kan makwabciyar Saudiyyar wato Yemen.

Karanta:  Donald Trump Na Fuskantar Suka Daga 'Yan Jam'iyyarsa

Amma kawo yanzu, gamayyar ta kasa taimaka wa shugaban Yemen, Abdrabbuh Mansour kwato yankunan baban birnin kasar, Sanaa daga hannun ‘yan tawaye.

Yana son rage dogaron kasar da man fetur

A watan Afrilun shekarar 2016, yariman mai karfin fada a ji, wanda kuma shi ne shugaban hukumar habaka tattalin arziki da cigaban Saudiyya, ya bayyana wani gagarumin sauyin da yake fatan zai kawo karshen dogaro da man fetur da kasar ke yi domin samun kudaden shiga.

Ya ce shirin da ake kira “Vision 2030” zai tabbatar kasar “za ta iya rayuwa ko babu man fetur.

Da wuya ya inganta dangantakar Saudiyya da Iran

A watan jiya sabon yariman ya musanta cewa Saudiyya za ta yi wata tattaunawa da abokiyar gabarta Iran.

Kasashen biyu na goyon bayan bangarorin da ke rikici a Syria da Yemen.

Dangantaka tsakanin Riyadh da Tehran ta kara tsami ne bayan da hukumomin Saudiyyan suka aiwatar da hukuncin kisa kan fitattccen malamin Shi’a, Nimr al-Nimr.

Kafofin watsa labaran Iran sun kira wannan karin girma “karamin juyin mulki”.

Yana da iyali

An haifi Mohammed bin Salman ne a ranar 31 ga watan Agustan 1985, kuma shi ne babban dan matar Sarki Salman ta uku, Fahdah bint Falah bin Sultan.

Ba kamar yadda aka saba ba, sabon yariman ya kammala dukkan karatunsa a cikin Saudiyya ne baki daya.

Ya yi karatun shari’a a jami’ar Sarki Saud gabannin kama aiki da wasu ma’aikatun gwamnati.

Mohammed bin Salman na da mata daya da ‘ya’ya hudu, biyu mata biyu maza.

Asalin Labari:

BBC Hausa

486total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.