Wani matashi ‘ya kashe mahaifinsa’ saboda aure a Jigawa

Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa a arewacin Nigeria ta gurfanar da wani matashi mai kimanin shekaru 25 bisa zarginsa da kashe mahaifinsa ta hanyar amfani da makami.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi cikin dare yayin da mahaifin wanda ake zargin mai kimanin shekaru 65 yake bacci.

Kakakin ‘yan sandan jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ya shaida wa BBC cewa binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa matashin ya kashe mahaifinsa ta hanyar buga masa fartanya da kuma itace bisa tsammanin yayansa ne.

Matashin mai suna Abdulhamid Abdullahi ya kullaci yayan nasa ne, bayan ya zarge shi da zuga mahaifinsu kan ya ki amincewa da yunkurin auren da Abdulhamid ke yi.

Su dai Magabatan Abdulhamid na nuna adawa da auren saboda ba shi da sana’a.

Lamarin dai ya fusata matashin, wanda ya yi yunkurin huce haushinsa a kan dan’uwansa, wanda shi kuma ya garzaya dakin mahaifinsu domin neman mafaka.

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce matashin ya bayyana mata cewa ya far wa mahaifinsu ne bisa kuskuren cewa yayansa yake duka.

Mahaifin Abdulhamid din wato Malam Abdullahi ya mutu bayan an garzaya da shi asibitin garin Nguru na jihar Yobe mai makwabtaka da Jigawa.

Matashin dai zai iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai idan kotu ta same shi da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Asalin Labari:

BBC Hausa

745total visits,1visits today


Karanta:  Jihar Jigawa Ta Gudanar Da Zabe Duk Da Kotu Ta Hana

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.