Wani soja ya fado daga jirgi mai saukar ungulu a Belgium

Dakaru na can suna neman gawar wani matukin jirgin soja a gabashin Belgium bayan ya fadi daga cikin jirgi mai sukar ungulu a lokacin atisayen sojin sama.

Dakaru uku sun dira daga jirgin samfurin Agusta A-109 da taimakon lema, ko da yake da matukin jirgin da mataimakinsa ba su da lema, in ji kafafen watsa labaran kasar.

Sun ce daya daga cikin matuka jirgin ya taimaka wa mutum uku yin tsalle suka fice daga cikinsa, kuma daga bisani sun ga babu kowa a kan kujerar matukin jirgin sannan tagar jirgin da ke bangarensa ta bude.

Ana yin faretin ne a Amay da ke kusa da Liège. Matukin jirgin ya fadi ne daruruwan mita daga wurin da ake yin faretin.

Har yanzu ba a san dalilin da ya sa matukin jirgin ya fado ba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

551total visits,1visits today


Karanta:  Alkali ya Yarharbi Wani ɗan Bindiga

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.