Wasu Manoma Sun Rasa Rayukansu a Wani Hadarin Kwale-kwale a Jihar Taraba

A cikin karamar hukumar Gassol dake jihar Taraba wasu manoma sun rasa rayukansu sanadiyar hadarin kwale kwale da ya rutsa dasu.

Yanzu haka dai rahotanni daga jihar Taraban sun tabbatar da cewa ana ci gaba da aikin ceto wasu mutane bayan da wani jirgin kwale-kwale ɗauke da wasu manoma ya kife, a wani kogi da da akewa lakabi da kwatan Nanido dake karamar hukumar Gassol.

Kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar a yau Litinin mutanen da lamarin ya rutsa da su manoma ne dake kan hanyarsu ta dawowa daga gona. Wani dan yankin ya ce an ceto akalla mutane hudu,yayin da aka samu gawarwaki shida,koda yake kawo yanzu ana cigaba da aikin ceto.

Shima da yake tabbatar da hatsarin kwale-kwalen Shugaban karamar hukumar Gassol din Hon.Yahuza Yayau,yace ya zuwa yanzu masu ceto na can na neman sauran wadanda ba’a gano ba.

To sai dai kakakin rundunan yansandan jihar Taraban ,David Misal yace ya zuwa yanzu jami’an yansandan yankin basu bada rahoton abun da ya faru ba,to amma yace zasu cigaba da bincikawa.

Wannan hatsarin jirgin kwale-kwalen na ma ko zuwa ne yayin da ake gargadin cewa akwai yuwuwaar samun ambaliya bana batun da yasa shugabanni yin gangamin fadakarwa.

Asalin Labari:

VOA Hausa

368total visits,2visits today


Karanta:  Musulmai da Kiristoci Sun Yi bikin Sallah da Gangamin Yiwa Shugaban Kasa Addu'a a Gombe

Leave a Reply

Your email address will not be published.