Wata mata da daba wa mijinta kwalba a Zamfara

Wata mata mai suna Hauwa’u ta daba wa mijinta kwalba a kirji da baya a yankin Filin Jirgi da ke Gusau a Jihar Zamfara.

Wata mata mai suna Hauwa’u ta daba wa mijinta kwalba a kirji da baya a yankin Filin Jirgi da ke Gusau a Jihar Zamfara.

Mai magana da yawun Asibitin kwararru na Yariman Bakura a Gusau, Auwal Usman Ruwan  Doruwa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce an kawo mutumin mai suna Bilyaminu Yusuf, kuma suna ci gaba da lura da shi kuma yana samun sauki.

Wata majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa ma’auratan sun yi aure shekara takwas da suka wuce, amma ba su samu haihuwa ba. Amma tun lokacin da ya ce zai kara aure, sai rikici ya fara bulla a gidan, inda har ta yi alwashin sai ta yi maganinsa. Sannan kuma ya ce matar ta gudu bayan ta aikata wannan aika-aikan.

Amma mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandar Jihar Zamfara, DSP Muhammad Shehu ya ce tuni suka kama Hauwa’u, kuma sun fara bincike a kan lamarin.

 

Asalin Labari:

Aminiya Dailytrust

1470total visits,1visits today


Karanta:  Gwamnatin Nigeria ce ta 35 a Afirka – Gidauniyar Mo Ibrahim

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.