Wata Sabuwar Cuta Na Lalata Gonaki a Jihar Filato

Wata sabuwar cutar tsiro da manoma suka kasa tantance ta, ta na lalata gonaki masu yawan gaske a jihar Plateau dake arewa maso tsakiyar Najeriya.

A cewar manoman, lamarin ya janyo masu hasara mai yawa, ganin irin barna da wannan cutar ke yi wa itatuwa kamar na gwaiba, mangwaro da sauran itatuwa a karamar hukumar Qua’an pan a jihar Plateau.

Manoman sun yi kira ga hukumomi da su kawo masu dauki don kawo karshen wannan sabuwar cuta da ke ci gaba da addabar gonakin nasu.

Shugaban sashen kula da lafiyar dabbobi a cibiyar binciken lafiyar dabbobi ta kasa dake Vom a jihar Plateau Farfesa Garba Hamidu Sharubutu, ya na cikin wadanda wannan sabuwar cutar ta addabi gonakinsu kuma ya yi wa wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka, Zainab Bababji bayanin barnar da wannan cutar ta yi wa gonarsa.

Wani mai shari’a Thomas Naron da gonarsa ta kamu da wannan cutar, shi ma ya yi kira ga hukumomi da su kawo daukin gaggawa domin ceto gonakinsu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

772total visits,3visits today


Karanta:  Kasuwar hannayen jari ta Nigeria ta yi matukar bunkasa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.