Willy Caballero: Chelsea ta sayi tsohon mai tsaron gidan Manchester City

Zakarun gasar Firimiya Chelasea ta sayi tsohon mai tsaron gidan Manchester City, Willy Caballero.

An sallami dan asalin kasar Ajentinan ne a lokacin da kontiginsa ya kare a karshen watan Yuni.

Caballero, mai shekara 35, ya je Ingila ne daga Malaga a shekarar 2014 kuma ya buga wasanni 26wa kungiyar Pep Guardiola a kakar bara.

Ya ce: “Na yi murnar komawa zakarun Ingila. Ina fatan haduwa da ‘yan wasan in kuma taimaka wa kungiyar domin ta sake samun nasarori.”

Chelsea ta sayar da mai tsaron gidan ta na biyu Asmir Begovic wa Bournemouth a watan Mayu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

709total visits,1visits today


Karanta:  Borussia Dortmund ta rasa inda Dembele yake

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.