‘Ya kamata masu kuɗi su biya wa talakawa inshora’

Majalisar wakilan Nijeriya ta gayyaci hukumar shirin inshorar lafiya na ƙasar NHIS, don yi mata bayani kan ƙarancin ‘yan Nijeriya da suka yi rijista da tsarin.

Nijeriya dai na da yawan al’umma kimanin miliyan 180, amma ƙasa da mutum miliyan uku ne kawai ke da inshorar lafiya.

Babban sakataren tsarin Farfesa Usman Yusuf ya ce kowanne mutum ya cancanci shiga tsarin inshorar lafiya ba sai lallai ma’aikata ba.

Ya ce suna da wani tsari mai suna VCSHIP wanda ta hanyar sanya naira 15,000 a shekara, mutum na iya cin gajiyar samun kulawar lafiya mafi dacewa.

“Yanzu idan ka kacaccala naira dubu goma sha biyar kullu yaumin wato naira arba’in da ɗaya ne.

To dubu goma sha biyar za ka iya zuwa asibiti ka ga likita har aiki a yi maka a dubu goma sha biyar. Ko (naira) miliyan aka caje ka, hukumata za ta biya.”

Farfesa Yusuf ya ce ko da yake, ba kowa ba ne zai iya ajiye wannan kuɗi a shekara ba, amma masu hali na iya biya wa masu ƙaramin ƙarfi.

Ya jama’a, kuna iya biya wa wasu (da ke da ƙaramin ƙarfi), in ji shi.

A cewarsa, ba wata ƙasa a duniya da za a ce gwamnati za ta iya ɗaukar nauyin kowa.

Har masallatai yake zuwa da sauran wuraren ibada don wayar da kan jama’a game da muhimmancin yin tanadi don samun kula da lafiya cikin rangwame.

Ya ce ya shafe tsawon shekaru a Amurka, “kuma ta fi kowa kuɗi a duniya. Ko ita ba ta iya ɗaukar nauyin kowa.”

Asalin Labari:

BBC Hausa

1147total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.