‘Yan Bindiga Sun Kashe Sifeton ‘Yan Sanda Da Kwamandan ‘Ya Sintiri Sun Kuma Yi Awon Gaba Da Mata 2

Wasu fusatattun ‘yan bindiga sun harbe har lahira wani sifeton ‘yan sanda da kwamandan ‘yan sintirin jihar Kaduna, haka kuma sunyi awon gaba da wasu ‘yan mata 2 a Unguwar Katsinawa, Shika cikin Karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Yayin da yake tabbatarwa gidan jaridar Daily trust faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mukhtar Hussaini Aliyu yace da safiyar ranar Lahdi ne ‘yan sandan suka ji kira layin karta kwana, inda cikin gaggawa suka baza jami’an su inda ake aika-aikar.

ASP Aliyu yace sifeton ‘yan sandan da kwamandan ‘yan sintirin sun ransa ransu a  yayin musayar wuta da ‘yan bindigar, inda kuma harsashin bindiga ya raunata wani kofur din ‘yan sanda.

Mahaifin kwamandan ‘yan sintirin, Malam Muhammad Gali, ya fadawa majiyar daily trust cewa ‘yan bindiga dauke da muggan makamai su kusan 50 sun yiwa gidan marigayin Malam Mustapha Muhammad Gali tsinke inda suka harbe shi har sau biyu suka kuma yi awan gaba da ‘ya’yansa mata biyu.

Ya karawa da cewa “Da misalin karfe dayan dare dana ya kira ni, ya fada min cewa ‘yan bindiga sun kewaye gidansa. Sai na tashi ‘yan uwansa daga bacci. Mun kusa zuwa gidan sai ‘yan bindigar suka fara harbin mu ta ko’ina.

Sai duka muka nemi gurin tserewa. Daga baya ne muka fahimci cewa an harbe shi an dauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Amadu Bello dake Shika inda daga baya ya rasa ransa. Yanzu abin da yafi damunmu shi ne ‘yan matan biyu da aka sace.”

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

471total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.