‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Yan Sanda 3 A Zamfara

Wasu mutanen da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace ‘yan sanda uku dake aiki a wata caji ofis din ‘yan sanda a garin Keta na Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

‘Yan bindigar  da har yanzu ba a san ko suwanene ba dauke da bundugu sun isa kyauyen inda suka kaiwa Caji Ofis din ‘Yan Sandan hari, har yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin hari ba.

An sami zaman lafiya a jihar ta Zamfara tun bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da gwamnatin jihar ta kulla a watan Desambar shekarar 2016 ta hannun shugabancin mataimakin gwamna jihar Ibrahim Wakkala Muhammad tsakanin ‘yan bindigar da ‘yan kato da gora.

Amma daga bisani wasu daga cikin ‘yan bindigar da ke son gurgunta waccen yarjejeniyar sun cigaba da kai muggan hare-hare kan wasu kyaukan jihar.

Ko kwanakin baya ma gwamnan jihar Abdulaziz Yari Abubakar ya bayyana damuwarsa kan hare-haren da ake yawan kaiwa wasu kyauyuka a jihar.

Inda yake cewa harin da wasu ‘yan bindiga suka kai ‘yan satuttukan da suka wuce a garin Bakura, Maradun da wasu yankunan karamar hukumar Anka abin Allah wadai ne wanda ba zasu taba amincewa dashi ba.

Tuni Shugaban Hurda da Jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Muhammad Shehu yace an baza shugaban caji ofis din garin na Tsafe da wasu ‘yan sanda domin neman ‘yan sandan da suka bata.

773total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.