‘Yan ci-rani 52 sun mutu a saharar Jamhuriyar Nijar

An gano gawar ‘yan ci-rani 52 wadanda suka mutu a tsakiyar saharar Jamhuriyar Nijar, kusa da Séguédine.

Rukunin ‘yan ci-rani 75 ke tafiya a cikin mota uku amma masu safarar mutane suka gudu suka bar su saboda tsoron haduwa da jami’an tsaro.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa an binne ‘yan ci-rani da dama, kuma na kai 23 daga wadanda suka tsira cikin gari, ko da yake daga bisani daya daga cikinsu ya mutu.

‘Yan ci-rani daga Afirka kan bi ta sahara zuwa Turai bayan sun wuce Libya da Bahar Rum.

Sai dai wannan tafiya na da matukar hatsari, domin kuwa akan makare su ne a cikin motocin a-kori-kura sannan kuma yawancinsu ba su da wani isasshen abinci.

Mako biyu da suka wuce, dakarun Jamhuriyar Nijar sun ceto ‘yan ci-rani 92 wadanda ke daf da mutuwa a Sahara.

An yi watsi da mutanen ne, wadanda suka hada da mata da kananan yara, ba tare da abinci da ruwan sha ba.

Asalin Labari:

BBC Hausa

729total visits,1visits today


Karanta:  An Damke Masu Safarar Mutane a Yammacin Afirka

One Response to "‘Yan ci-rani 52 sun mutu a saharar Jamhuriyar Nijar"

  1. Fatsuma Musa Magaji   July 5, 2017 at 6:00 am

    Subhannallah Allah Ya jikansu. Amin

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.