‘Yan jam’iyyar PDP da APC sun ziyarci Buhari

Shugabannin babbar jam'iyyar adawa ta PDP da na jam'iyyar APC mai mulki suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a fadar gwamnati da ke Abuja.

A yau  Juma’a ga watan Agusta shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP da na jam’iyyar APC mai mulki suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a fadar gwamnati da ke Abuja.

Tawagogin sun kai ziyarar ne a lokaci daya da misalin karfe 11 na safe, inda Ahmed Makarfi shugaban jam’iyyar PDP ya jagoranci tawagarsa, John Odigie-Oyegun na jam’iyyar APC kuma ya jagoranci tasa tawagar.

Da yake jawabin yi musu maraba, Shugaba Buhari ya nuna matukar godiyarsa da suka samu lokaci duk da irin ayyukan da ke gabansu, suka je yi masa maraba da dawowa gida.

“Wannan ziyara na nuna cewa Najeriya kasa daya ce mai hadin kai. Ba taron jam’iyya ba ne. Ba taron siyasa ba ne. Alama ce ta hadin kan kasa. Wannan na nuna cewa dimokradiyyarmu ta halin girma ce,” in ji Shugaba Buhari.

Ya kara da cewa, “”Dimkoradiyyar jam’iyyu da yawa ….. Adawa ba ta nufin tashin hankali ko kiyayya ko gaba. Dimkoradiyya na bukatar bangaren hamayya mai karfi amma mai sanin ya kamata.

Asalin Labari:

BBC HAUSA

603total visits,1visits today


Karanta:  Halin da muka samu Shugaba Buhari a ciki — Rochas Okorocha

Leave a Reply

Your email address will not be published.